Labarai

Mayaƙan ISWAP Da Boko Haram 41 Sun Mutu A Wani Faɗa Tsakanin Su

 

Kwamandoji da mayakan ISWASP da na Boko Haram 41 ne aka tabbatar sun mutu a wani kazamin fada tsakanin kungiyoyin ta’addancin a wani hari da ISWAP ta kai wa Boko Haram.

’Yan ta’addan sun ba hamata iska ne a yankin Duguri na Karamar Hukumar Kukawa na Jihar Borno, inda mayakan ISWAP da wani kwamandansu mai suna Bakura Buduma ya jagorance su suka far wa Boko Haram.

Tabbatattun majiyoyi sn ruwaito cewa bangarorin biyu sun yi wa juna barna, inda mayakan da kwamnadojinsu suka sheka lahira a musayar wutar.

Shi ma da yake tabbatar da hakan, Zagazola, kwararre kan abin da ya yaki da ta’addanci a yankin Tafkin Chadi, ya ce ISWAP ta fi yi wa Boko Haram barna, inda ta kashe kwamandojinta kusan goma a fadan.

A baya-bayan nan kungiyoyin biyu na yawan kai wa juna hari a dazukan Jihar Borno da yankin tafkin Chadi, kuma suna wa juna mummunar lahani.

Aminiya ta kawo rahoton yadda a kwanakin baya rikicin kabilanci a cikin kungiyar Boko Haram ya yi ajalin mayakanta da kwamandoji 82 lokaci guda.

Rahotanni sun nuna yanzu ISWAP ce ke samun galaba a kan Boko Haram bayan sauya sheka da wani babban kwamandanta Abou Idris ya yi daga Boko Haram.

Jaridar Aminiya

Leave a Reply