Home Labarai Mutum 1,715 ƴan bindiga suka kashe cikin wata uku a Najeriya, cewar...

Mutum 1,715 ƴan bindiga suka kashe cikin wata uku a Najeriya, cewar wani Rahoto

Wani rahoto na kamfanin Beacon Consulting mai nazari kan tsaro a Najeriya ya ce ƴan bindiga sun hallaka mutum 1,715 a faɗin Najeriya tsakanin watan Yuli zuwa Satumban 2023.

A cikin rahoton wanda kamfanin ya fitar yau Alhamis, ya ce an kashe mutane mafi yawa ne a yankin arewa maso gabashin ƙasar, inda aka kashe mutum 491.

Sai kuma yankin arewa masotsakiyar ƙasar inda aka kashe mutum 366.

Arewa maso yammacin ƙasar ne na uku a yawna mutanen da aka kashe, inda aka kashe mutum 362.

Jihohin da lamarin ya fi muni su ne Borno da Filato da kuma Zamfara.

Najeriya dai na fama da matsalolin tsaro a yankunan daban-daban na ƙasar, waɗanda suka haɗa da na ƴan fashin daji a arewa maso gabas da Boko Haram a arewa maso gabashin ƙasar.

Bugu da ƙari ana fama da matsalar ƴan fashi da kuma masu garkuwa da mutane a arewa maso tsakiya da kuma kudancin ƙasar.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.