Labarai

Rasha Ta Yi Ruwan Bama-Bamai A Masallacin Da Sama Da Mutum 80 Suka Fake A Ukraine

Dakarun Rasha sun jefa bama-bamai a wani masallaci da ke birnin Mariupol na Kudancin kasar Ukraine, inda sama da fararen hula 80 suka nemi mafaka.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Ukraine ce ta tabbatar da hakan a shafinta na Twitter ranar Asabar, inda ta ce daga cikin wadanda ke cikin masallacin har da ’yan kasar Turkiyya da suka fake a ciki.

“Masallacin Sultan Suleiman da matarsa Roxolana (Hurrem Sultan) ya sha ruwan bama-bamai daga dakarun Rasha. Sama da mutum 80 ne, cikinsu har da mata da kananan yara suka mutu, bayan sun samu mafaka a cikinsa, cikin har da ’yan Turkiyya,” inji Ma’aikatar ta Ukraine.

Sa dai ba ta bayyana ko mutanen sun rasa ransu ba ko kuma m raunuka suka samu.

Aminiya ta ce sai dai hukumomin kasar ta Rasha sun musanta kai hari a kan fararen hula, a abin da ta bayyana da aikin soja a Ukraine.

Ukraine dai ta zargi Rasha da toshe hanyoyin birnin na Mariupol, inda dubban daruruwan mutane suke ciki, ko da yake Rashar na zargin Ukraine da gazawa wajen kwashe mutanen.

Kusan mako biyu ke nan birnin na Mariupol shan ruwan albarusai da bama-bamai bayan dakarun Rasha sun yi masa kawanya.

Ministan Harkokin Wajen Ukraine, Dmytro Kuleba ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Juma’a cewa, “Kawanyar da aka yi wa birnin Mariupol ita ce babbar lefin keta hakkin dan Adam a duniya. Fararen hula 1,582 ne suka mutu cikin kwana 12.”

Leave a Reply