Labarai

Rikici ya ɓarke tsakanin ƴan sanda da jami’an shige da fice  a Maiduguri 

 

Jami’an ’yan sanda da na shige da fice a rukunin gidaje na 777 da ke Maiduguri babban birnin jihar Borno, sun ba hammata iska a ranar Juma’a.

Rikicin dai ya haifar da harba bindigogi daban-daban wadda hakan ya haifar da fargaba a tsakanin mazauna wajen da lamarin ya faru.

Rikicin ya faru ne a ofishin ’yan sanda da ke cikin rukunin gidajen da ke gefen hanyar Maiduguri zuwa Kano, saboda takaddama kan wani ofishi.

Jami’an Hukumar Kula da Shige da Fice ta Kasa (NIS) ta mamaye wannan sansanin tun a shekarar 2014, saboda watsi da rundunar ’yan sandan ta yi da shi bayan hare-haren da ake kai wa jami’an tsaro daga ’yan ta’addan Boko Haram.

A kwanakin baya, Kwamishinan ’Yan sandan jihar Borno, Muhammed Yusuf, ya umarci jami’an ’yan sanda reshen da su kwato duk wuraren da ’yan sandan suka yi watsi da su a wani shiri na inganta tsaro a birnin.

Wani jami’in dan sanda a lokacin da yake magana da masanin nan kan yaki da ta’addanci, Zagazola Makama, ya bayyana cewa, jami’an ’yan sanda reshen Bulunkutu sun kudiri aniyar kwato ofishin daga hannun jami’an shige-da-fice.

Sai dai yunkurin nasu ya haifar da rudani yayin da jami’an NIS suka hana su shiga.

Ya ce jami’an shige da ficen sun yi mamakin mamayar da aka yi da safe ba tare da wata sanarwa ba, wadda hakan ya sa suka yanke shawarar ba za su bar ofishin ba, duk da cewa an sanya shi da alamar ’yan sandan Najeriya

Lamarin dai ya ta’azzara ne lokacin da bangarorin biyu suka fara harba bindigoginsu a sama, lamarin da ya haifar da firgici a tsakanin mazauna rukunin gidajen 777 da ke birnin na Maiduguri.

Rahotonni sun  ce da yawa daga cikin mazauna rukunin gidajen wadanda a baya suka fuskanci irin wannan lamari sakamakon rikicin Boko Haram sun rika guduwa don tsira da rayukansu.

Daga karshe dai sojojin Najeriyar da ke kusa da runduna ta 33 ne suka daidaita lamarin inda suka kwantar da rikicin.

Jaridar Aminiya