Latest:
Labarai

Rundunar Ƴan Sandan Najeriya Ta Kai Samame Maboyar ƴan IPOB

Rundunar Ƴan sandan Najeriya sun ce sun kai samame a wata cibiyar da ake hada bama-bamai a jihar Imo da ke kudu maso gabashin kasar, inda ake ci gaba da samun tashin hankalin ƴan aware.

Sun ce samamen ya faru ne a ranar Laraba a garin Umuaka bayan an kwarmata ma su bayanan sirri.

Mai magana da yawun ƴan sandan ya ce an kwarmata ma su wata maɓoyar da masu fafutikar kafa ƙasar Biafra IPOB, ke ƙera abubuwan fashewa.

Ya ce sun kama wani da ake zargi tare da kwato kayayyaki da suka haɗa da bututun karfe fiye da 50.

Hukumomin Najeriya na ɗora alhakin hare-haren baya-bayan nan kan ƴan ƙungiyar IPOB mai fafutukar kafa wata ƙasa ta ƴan kabilar Igbo.

Leave a Reply