Skip to content
September 14, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • News

Rundunar ‘Yan Sanda ta Bauchi ta Cafke Wani Sanannen Mai Fasa Kwalban Wutar Lantarki, Ta Gano Kayan da Aka Sata

July 30, 2025 2 minutes read

Daga Abdulaziz Garba

Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Bauchi ta cafke wani mutum mai suna Kabiru Bala, ɗan shekara 31 da haihuwa, bisa zargin aikata laifuffukan sata da lalata kayan gwamnati a sassa daban-daban na jihar.

Wanda ake zargin, mazaunin ƙaramar hukumar Darazo ne, an kama shi ne bayan wani korafi da wani mai suna Dr. Auwal Abdullahi daga jihar Gombe ya shigar. A cewar ‘yan sanda, Dr. Abdullahi ya ce a ranar 20 ga Yuli, 2025, da misalin ƙarfe 8:30 na safe, ya ajiye motarsa kirar Peugeot 307 mai lamba ABJ-982NC a masaukin da ke otal din Al-Umma Village Lodge, inda ya kama ɗaki.

Da safiyar washegari, ya tarar da cewa an fasa gilashin motar tare da sace kayayyaki masu muhimmanci ciki har da:

Tsabar kudi har Naira Miliyan Biyar (N5,000,000)

Kwamfutar tafi-da-gidank

Waya kirar Tecno Smart 17

Bayan samun rahoton ne, rundunar ‘yan sanda ta fara bincike cikin gaggawa ta hanyar amfani da fasahar zamani, wanda hakan ya kai ga kama Kabiru Bala. A lokacin da ake tuhumarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, tare da bayyana yadda ya dade yana aikata laifin satar wayoyin lantarki a wurare kamar su Alkaleri, Ningi, Darazo (Kari da Lanzai), da cikin garin Bauchi.

Ya bayyana cewa yana siyar da wayoyin wutar da ya sace bisa nauyinsu, inda ake saya Naira dubu goma (N10,000) akan kowanne kilo. A baya, ya siyar da kilo shida (6kg) inda ya samu Naira dubu sittin (N60,000). Ya ƙara da cewa ya dade yana aikata irin wannan laifi tsawon kusan shekaru bakwai, kuma an kama shi sau takwas, inda ya sha zuwa gidan gyaran hali.

An kuma gano wasu daga cikin kayayyakin da aka sace a hannunsa, waɗanda suka haɗa da kwamfutar tafi-da-gidanka da wayar Tecno Smart 17.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya tabbatar da kama wanda ake zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.

Wakil ya ƙara da cewa rundunar tana ci gaba da bincike tare da kokarin kama sauran abokan haɗin gwiwa da masu sayen kayan da ake sacewa.

Tags: Bauchi State Government Bauchi state police command Jos Electricity Distribution Company Nigeria Security and Civil Defence Corps (NSCDC)

Post navigation

Previous: BASEPA, WaterAid Partner to Train Environmental Health Officers on Digital Sanitation Tools
Next: Next Post

Related Stories

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.