Babban mai bai wa shugaban Najeriya shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu ya ce matsalar satar danyen man fetur ce ta kara tsadar rayuwa a kasar.
Malam Nuhu Ribadu ya fadi haka ne yayin cewa Najeriya na asarar gangar danyen mai 400,000 duk rana sakamakon ayyukan ɓarayin man na ciki da wajen ƙasar, duk kuwa da ƙoƙarin da gwamnati ke yi na kawar da matsalar ɓarayin man.
Ribadu ya bayyana haka a lokacin da ya jagoranci tawagar da shugaban ƙasa ya aike zuwa duba wasu wurare na man fetur da iskar gas a yankin Owaza na Jihar Abiya da kuma Odogwa na Karamar Hukumar Etche da ke Jihar Ribas.
Da yake jawabi a gaban manema labarai a ranar Asabar, Ribadu ya ce ayyukan masu satar ɗanyen mai da ke fasa bututan mai na kawo wa ƙasar babban naƙasu ta fuskar tattalin arziki, lamarin da ya ce shi ke haifar da tsadar rayuwa a ƙasar.
“Abin takaici ne yadda wasu tsirarun mutane ke sace albarkatun ƙasarmu domin amfanar da kawunansu, abin da kuma ke haifar da asara mai yawa ga ƙasarmu da mutanen yankin.”
Ya ƙara da cewa “Najeriya na da arzikin man da za ta iya haƙo gangar mai miliyan biyu a kowacce rana, amma yanzu ƙasa da ganga miliyan 1.6 kawai muke iya haƙowa, sakamakon ayyukan ɓarayin mai da masu fasa bututan man.”
“Kenan kusan gangar mai 400,000 wasu ɓata-gari da masu yi wa tattalin arzikinmu zagon-ƙasa ke sacewa a kowacce rana domin amfanar da kansu,” in ji Ribadu.
Mai bai wa shugaban ƙasar shawara kan harkar tsaro ya ce darajar gangar mai 400,000 a yanzu ta kai dala miliyan hudu, “kenan waɗannan kuɗaɗe muke asara a kowacce rana sakamakon ayyukan waɗannan ɓata-garin.”
“Idan ka lissafa dala miliyan huɗu sau kwanakin shekara 365, za ka ga cewa maƙudan biliyoyin daloli muke asara a kowacce shekara.”
Kuɗin da ya ce sun isa ƙasar inganta tattalin arzikinta ta hanyar farfaɗo da darajar ƙudin ƙasar, da rage tsadar rayuwa da sauran fannoni.
Ribadu ya ƙara da cewa gwamnatin Shugaba Tinubu na damuwa da wannan mummunar ɗabi’a, ya kuma ce gwamnatin ta fara ɗaukar matakai don kawo ƙarshen wannan matsala.
Jaridar Aminiya
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.