Siyasa

Shugaban Jam’iyyar APC Ya Nuna Damuwa Kan Yadda Ake Ficewa Daga Jam’iyyar

Shugaban jam’iyyar APC mai mulki Abdullahi Adamu ya ce ya damu matuka, kan yadda ake barin jam’iyyar.

Sanatoci bakwai ne suka sauya sheka daga APC zuwa wasu jam’iyyun, bayan sun kasa samun tikitin tsayawa takara a jam’iyyar a zaben 2023.

Sanatocin da suka fice daga APC sun hada da tsohon gwamnan Kano Ibrahim Shekarau, da Yahaya Abdullahi daga jihar Kebbi, da Halliru Dauda Jika daga jihar Bauchi da kuma Ahmad Babba Kaita daga jihar Katsina.

Sauran sun hada da Lawal Yahaya Gamau daga Bauchi, sai Francis Alimikhena daga jihar Edo.

Da yake ganawa da manema labarai bayan wata ganawar sirri da Sanatocin jam’iyyar, Mista Adamu ya ce akmbin takaici ne yadda yan majalisar ke ficewa daga jam’iyyar.

” Ban damu da abinda ke faruwa a wata jam’iyya ba, damuwa ta itace abinda ke faruwa a jam’iyyata.”

” Babu Shugaba nagari da ba zai damu ba idan ya rasa mamba ko da daya ne a jam’iyyarsa, ballantana ayi maganar mamba biyu, ko uku.”, in ji shi.

Sai dai Shugaban na APC yace suna kan tattauna hanyar da zasu dinke wannan baraka ta ficewa daga jam’iyyar, duk da ya ce ba wani sabon abu bane.

Leave a Reply