Labarai

Sojoji Sun Hallaka Ƴan Ta’adda 113, Sun Cafke 300, tare da Ceto Mutane 91 Da Aka Yi Garkuwa Da Su

 

Hedikwatar tsaro ta kasa a ranar Alhamis ta ce, sojoji sun kashe ‘yan ta’adda 113, sun cafke ‘yan ta’adda 300, tare da ceto mutane 91 da aka yi garkuwa da su a cikin mako guda.

Daraktan ayyukan yada labarai na tsaro, Manjo Janar Edward Buba wanda ya bayyana hakan, ya ce, sojoji sun kama mutane 25 da ake zargin barayin danyen man fetur ne tare da lalata haramtacciyar matatar man fetur 49 sannan kuma sun kama kayayyakin da aka tace da darajarsu ta kai Naira Miliyan N571.

Ya ce, sojojin sun kwato makamai iri daban-daban har 129 da alburusai kala daban-daban 717.

Ya kara da cewa, rundunar sojin kasar za ta ci gaba da tasa keyar ‘yan ta’adda da kungiyoyin da ke neman dakile duk wani ci gaba na zaman lafiya da tsaro a kasar.

Jaridar Leadership