Labarai

Wajibi A Tabbatar Da Adalci Wajen Hukunta Wanda Ya Kashe Goni Aisami

Published by Abdullahi Yahaya

Shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawal yayi Kira ga hukumomin tsaro musamman rundunar yansanda data tabbatar da adalci wajen gaggauta hukunta wadanda ke da hannu na kashe malamin addinin musulunci nan na jihar Yobe ,Sheikh Goni Aisami, Wanda ake zargin wani jami’in soja da kashe shi a Ranar jumaar data shige.

Lawal yayi wannan kiran ne lokacin da yakai ziyarar taaziya ga iyalan marigayin a garin Gashua dake jihar Yoben, a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai tallafa masa kan kafafen watsa labarai, Ola Awoniyi.

Shugaban majalisar dattawan da tawagarsa sun yi adduar Allah ya jikan marigayin.

Lawan Wanda ya bayyana marigayi amatsayin Wanda ya taba zama Mai bashi shawara kan harkokin addini tare da tabbatar da cewar za’a cigaba da bibiyar wannan shariar har Sai an tabbatar anyi adalci wajen yanke hukunci.

About the author

Abdullahi Yahaya

Seasoned Blogger. Software Developer. Web Designer & Developer. Cybersecurity Expert. Database Engineer. IT Enthusiast.

Leave a Comment