A karon farko sojojin da suka yi juyin mulki a Nijar sun bayar da dama likita ya gana da Shugaba Mohamed Bazoum a ranar Asabar.
Kamfanin dillancin labaran AFP ya ruwaito daya daga cikin mutanen da likitan ya tafi da su yana cewa likitan ya kai wa shugaban da iyalansa wadanda suke tsare tare abinci.
Hakan na faruwa ne kwana guda bayan sakataren harkokin wajen Amurka ya ce sojojin da suka yi juyin mulkin sun ki sakin iyalan Bazoum.
Dama dai Bazoum ya yi korafin cewa busashiyar shinkafa da taliya sojojin suke ba shi.
A Lahadin da ta gabata ne dai wa’adin da ECOWAS ta bai wa sojojin kasar na su mika mulki ga farar hula ya kawo karshe, wanda bayan hakan ne ECOWAS din ta bukaci dakarunta da su daura damarar yaki.
TRT Afrika Hausa
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.