Home Labarai ‘Yan sanda sun garkame Majalisar dokokin Jihar Nasarawa kan rikicin shugabanci

‘Yan sanda sun garkame Majalisar dokokin Jihar Nasarawa kan rikicin shugabanci

Rundunar ‘yan sandan Najeriya reshen Jihar Nasarawa ta rufe Majalisar Dokokin jihar “don gudun rikici” bayan an samu ɓangare biyu na ‘yan majalisar da ke adawa da juna.

A ranar Talata ɓangare ɗaya ya zaɓi Daniel Ogazi a matsayin kakakin Majalisar, yayin da ɗaya tsagin suka zaɓi Ibrahim Balarabe.

Kakakin ‘yan sandan jihar, DSP Ramhan Nansel, ya faɗa wa Gidan Rediyon Tarayya na Najeriya cewa Kwamashinan ‘Yan Sanda Maiyaki Baba ne ya ba da umarnin rufe Majalisar bayan tattaunawa da sauran masana tsaro.

“Ba za a bar kowane ɓangare ya shiga Majalisar ba har sai ƙura ta lafa,” in ji shi.

An tsara za a rantsar da sabuwar Majalisar ta bakwai a ranar Talata amma aka ɗaga zaman sakamakon rikicin.

BBC Hausa


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.