Labarai

Za’a Rateye Dan Sandan Da Ya Kashe Wani Kan Naira Dari

Wata babbar kotu a birnin Fatakwal na Jihar Ribas ta yanke hukuncin kisa kan wani tsohon jami’in ɗan sanda bisa samun sa da kashe wani direban motar bas saboda cin hancin naira 100 a shekarar 2015.

A lokacin da take yanke hukunci, mai shari’a Elsie Thompson ta ce shaidun da aka gabatar a gaban kotu sun nuna cewa tsohon sajan ɗin James Imhalu ya yi harbin bindiga da gangan kan direbar motar hayan, David Legbara tare da kashe shi nan take.

Mai shari’a ta bayyana tsohon sajan din James Imhalu a matsayin makashin da bai kamata a bar shi ya ci gaba da rayuwa ba a cikin al’umma.

Ta kara da cewa kotun ta samu tsohon ɗan sandan da laifi saboda amsa tuhuma kan abin da aka aikata da shaidun da aka gabatar a kansa.

Lauyan da ke shigar da kara, Kingsley Briggs ya yaba da hukunci wanda ya ce zai kwantar da hankalin iyalan mamacin kasance kuma shi ne mai kula da iyayensa.

Leave a Reply