National NewsSiyasa

Zaben Fidda Gwani: Tambuwal Ya Janye Wa Atiku

Gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal ya janye takararsa inda ya buƙaci magoya bayansa su marawa tsohon mataimakin shugaban ƙasa Alhaji Atiku Abubakar.

Tambuwal ya sanar da janye wa ne bayan wakilai daga jihohin Najeriya sun fara kaɗa ƙuri’a a zaɓen fitar ɗan takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar PDP mai hammaya.

Haka kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar din ya gode wa gwamnan jihar Sokoto Aminu Waziri Tambuwal wanda ya janye takararsa kuma ya sanar da mara masa baya.

A sakon da ya wallafa a Twitter, Atiku ya ce yana fatan yin aiki da Tambuwal domin hada kan PDP da Najeriya baki daya.

 

 

 

Leave a Reply