Labarai

Zamuyi wasan kwallon kafa da dukkanin yan dabar jihar Kano domin samun fahimtar juna a tsakanin mu -Kwaminishinan yan sandan Kano.

Daga Ibrahim Aminu Riminkebe, Kano.

Rundunar Ƴan sandan jihar za ta shirya wasan kwallon kafa ga kungiyoyin ƴan dabar da suka amince da tayin da ta musu na ajiye makamai domin rungumar zaman lafiya.

Kwamishinan Ƴan sandan jahar Kano CP Muhammad Ussaini Gumel ne , ya bayyana hakan da a taron manaima labarai daya gudana a shelkwatar rundunar dake Bompai Kano.

Rundunar ƴan sandan ta gabatar da waɗanda ake zargi da aikata laifuka mabanbanta su 108 da aka cafke su ƙasa makonni uku.

CP Gumel ya ƙara da cewa sun kafa masu garkuwa da mutane 3, Ƴan fashi da makami 24, Dilolin ƙwaya 24, Ɓarayi 9.

Sauran sun haɗa da Ɓarayin motoci su 2 , Ɓarayin Adaidaita Sahu 3 da kuma ɓarayin Babura 3, sai ƴan daba su 57 da ƴan damfara 5.

Rundunar ta samu nasarar bindigu 5 ciki harda ƙirar gida guda 2, sai harsasai , babura 2 ,Adaidaita sahu 4 da motoci 6 da kuma wayoyin salula 11.

Sauran sune Shanu 2, sinƙi-sinƙi na Tabar Wiwi 132, Ƙwayar Diazepam 167, Exol 170, Adduna 36 da Wuƙaƙe 20.

Haka zalika rundunar ta yi nasarar dawo da Zoɓo buhuna 12, sai Almakashi, Guduma da daidai sauransu.

Kwamishinan ƴan sandan jahar Kano ya godewa al’ummar jahar bisa haɗin kan da suke basu akoda yaushe.

Leave a Reply