Labarai

Zulum Ya Ziyarci Iyalan Masu Kamun Kifi Da Yan Ta’ada Su Ka Hallaka A Borno

Gwamana Babagana Umara Zulum na jihar Borno ya ziyarci iyalan masu kamun kifi guda 30 wadan da yan ta’addan Boko Haram suka hallaka a ranar laraban nan a kauyen Muldolo wanda ke karamar hukumar Ngala na jihar.

Gwamna Zulum ya kasance a yankin Dikwa inda masu kamun kifin suke zaune sukan kumayi sana’ar kamun kifi ne a yankin Mukdolo kafin daga bisani akayi musu kwantan Bauna.

Gwamnan ya gana da dukkanin iyalan masu kamun kifin a fadar Shehun Dikwa Alhaji Ibrahim Ibn Ibrahim El-Kanemi.

Karanta: APC Ta Bukaci Ganawa Da Tinubu, Kashim, Sanatoci, Yan Majalisan Wakilai

Yace a madadin gwamnati da kuma al’umar gari , ya mika sakon ta’aziyyarsa wa iyalai da yan uwan da abin ya shafa , Yakuma bukace su dasu maida komai zuwa ga Allah , yace shi kadai zai iya yin hisabi a gidan duniya dakuma ranar gobe.

Gwamna Zulum Yakuma gabatar da kayayyakin tallafi wa kowanni iyalan da suka rasa yan uwansu, Yakuma tabbatar musu da cewa zai cigaba da tallafa musu a kowanni lokaci.

Shima a nasa bangare Shehun Dikwa ya mika sakon godiyarsa wa gwamna Zulum amadadin al’umar yankin Yakuma yi addu’ar Allah ya basu hakuri Yakuma saka masa da Alkhairi.

Leave a Reply