Usman Abdullahi Koli
A lokacin da mutane da dama ke cike da fargabar rikicin cikin gida da ka iya Éarkewa ya kuma haifar da rarrabuwar kai a tsakanin manyan âyan siyasar jihar Bauchi, lokacin ne da ake sauya fasalin siyasa a matakin Æasa da jihohi, sai ga wani mutum da ya zo da manufar haÉa kan jamaâa da samar da hanya mai Éullewa, musamman bayan zaÉukan da suka gabata.
Yanayin siyasa, musamman na Jihar Bauchi, ya saba da rikice-rikice da nuna son zuciya daga wasu tsirarun masu ruwa da tsaki. Yayin da jihar ke fuskantar Æalubale da dama da ke buÆatar gyara cikin gaggawa da Æwarewa, tambayar ita ce: wa zai iya cimma waÉannan kyawawan manufofi? A nan ne ya kamata mu duba dacewar Bala Wunti a wannan lokaci mai sarÆaÆiya.
Daga cikin âyan siyasa da suka fito zawarcin kujerar gwamnan Bauchi a kakar zaÉen bana, babban abin da ya kamata a duba shine haÉin kai bisa kyakkyawar manufar ceto alâummar jihar, a fitar da tsarin yaÆar talauci, rashin tsaro, yunwa, rashin aikin yi, da sauran matsalolin da ke hana mu ci gaba da gogayya da sauran jihohin da suka yi mana fintinkau.
Akwai wasu mutane da shigar su siyasa na iya kawo mafitar da ma hukumomi suka gaza samarwa tsawon lokaci. Halayensu kuma na sa har masu kallonsu cike da shakku su yarda cewa har yanzu nagarta na da muhimmanci musamman ga jagororin jamaâa. Dr. Bala Maijamaâa Wunti na daga cikin irin waÉannan mutane. Labarinsa ba na tashen dare Éaya ba ne, labari ne na yadda rayuwa ta ginu bisa Æalubale, faÉi-tashi da jajircewa duk rintsi, kuma aka Éora ta bisa ginshiÆin gaskiya, jin Æai da kishin alâumma tun farko.
Fitowarsa daga tsatson masu Æaramin Æarfi ya sa rayuwa ba ta hannanta masa damammaki cikin sauÆi ba, hasali ma dai, tun wuri ta yi tsananin da ta tilasta masa zama mai juriya, ya kuma koyi dogaro da kai. Kowane mataki na rayuwarsa cike yake da rashin tabbas, sai dai hakan bai sa ya zama mugu, ko wanda zuciyarsa ke cike da Æunci da kyashi ba, sai ya koyi haÆuri, tausayi, da nutsuwa yayin da alâamura suka rincaÉe. Inda wasu kan gigice, yakan tsaya cike da nutsuwa. Wannan wata kyakkyawar Éabiâa ce da ake buÆatar shugabanni da ita.
*Tarihin Rayuwa da Aiki*
Neman ilimi da Bala Maijamaâa Wunti ya bi irin tafarkin da rayuwarsa ta faro a kai, zango ne na jajircewa da fuskantar Æalubale. Daga karatun Chemistry a Jamiâar Ahmadu Bello, zuwa samun horo a fannin gudanarwa a Jamiâar Abubakar Tafawa Balewa da Æarin kwasa-kwasai a wurare da dama, kowane mataki alama ce ta sadaukarwa. Abin da wannan gwagwarmaya ta samar ba mutum mai ilimi ba ne kaÉai, ta samar da mutum mai fahimta, wanda ya san sarÆaÆiyar alâamura, yake mutunta tsarin gudanarwa, kuma yake girmama hangen nesa. A duniyar da ake gaggawa, ya zaÉi bin doguwar hanyar cimma nagarta, wannan kuma ya shafi kowane Éangare na rayuwa da aikinsa.
Lokacin da ya fara aiki da Kamfanin Mai na Æasa wato NNPC Limited a 1994, ya tsinci kansa a Éaya daga cikin maâaikatu mafi tsauri a Æasar nan. Duk wani alheri da ke tattare da sunansa a yau, ba daga sama ya zo ba, Daga matsayinsa na farko na Production Programming Officer har zuwa Chief Upstream Investment Officer, tafiyarsa ta nuna ci gaba da ya wanzu bisa Æwarewa, ba surutu da bambaÉanci ba. Ya fahimci tsarin ciki da bai, ya gane matsalolinsa, kuma ya zaÉi kawo gyara, ba zama Éan kallo kawai ba. Yayin da wasu ke neman suna, ya samar wa kansa gurbin zama bisa Æwarewa. Yayin da wasu suka bazama neman muÆamai da sarautu, shi ya tsaya domin samun gogewa a fagen jagoranci da warware matsaloli.
Nauyin gudummuwar da ya bayar a fannin mai da iskar gas a bayyane yake a maâauni na zahiri a idon masu bibiyar alâamura. Ya taka rawar gani wajen Æarfafa tsarin zuba jari, dawo da tsarin aiki bisa kwarewa, da gyara ayyukan da suka daÉe suna gudana ba tare da tabbataccen tsari ba. Shirye-shirye da ya aiwatar irin su Operation White ba garambuwal ga fannin aiki da fasahar zamani kawai suka yi ba, sun kuma nuna cewa ana iya samun gaskiya da riÆon amana ko da a wurare masu rikitarwa. A wannan wuri da kowace shawara ke tasiri ga rayuwar duk wani Éan Æasa, salon gudanar da aikin sa ya kasance cikin natsuwa da hangen nesa, ya fifita ribar da za ta mamaye koâina a tafiya mai dogon zango, saÉanin masu azarÉaÉin da kan nemi yabo cikin ÆanÆanin lokaci. Wannan shi ne bambanci tsakanin masu tafiyar da tsarin da suka tarar da masu Æarfin hali da ilimin sauya shi zuwa tsari mafi kyau, mai Éorewa.
TaÆaita rayuwarsa ga nasarorinsa a aikin gwamnati kaÉai tamkar cin tuwo ne babu miya. Abin da ya bambanta Bala Wunti da sauran mutane ba wai abin da ya yi a maâaikatun gwamnati ba ne, har da abin da ya yi a wajen su, wanda kuma wannan shi ne Éangaren da alâummarsa ta fi tasirantuwa da nasararsa. Hausawa na cewa Éan halas ba ya manta mafari, don haka Bala Wunti bai manta wahalhalun da ya sha a rayuwa ba, sun zamar masa fitila wajen haska buÆatun alâumma, tare da ba shi Æaimin ÆoÆarin magance damuwarsu. Sanin inda ya fito, da yadda ya taso yana tasiri kan yadda yake muâamalantar mutane, da kuma yadda yake jajircewa wajen tallafa wa mabuÆata gabas da yamma, kudu da arewa. Ba kuma tallafin wucin-gadi yake bayarwa ba, taimakon mabuÆata wani Éangare ne na rayuwarsa ta yau da kullum. Æalibai da dama sun amfana, alâumma sun samu ci gaba, mabuÆata na samun taimako, kuma duk cikin sirri da mutuntawa ba tare da hayaniya ko gori ba. Tallafin da ya bayar ga Éaliban makarantun gaba da sakandare ba tallafi falle Éaya ba ne, aâa, alâadarsa ce. Wasu mutanen suna bayarwa a lokacin da bayarwa ke da sauÆi. Shi yana bayarwa ne saboda yana ganin hakan wajibi ne, domin tallafar alâummarsa.
Sannan Éabiâunsa ma ababen koyi ne, musamman ga matasa. Ba ya shiga sharo ba shanu. Ba ya sayar da âyancinsa don ribar rana Éaya, yana ganin hakan a matsayin cin dare Éaya. A yankin da a tsarin siyasa da aiki inda ake Éaukar sassaucin raâayi a matsayin hikima saboda ba a san inda rana za ta faÉi ba, irin tsayuwar daka da yake yi kan abin da ya yi amanna da shi wani nauâi ne na jarumta, ta yadda duk wanda ya bi shi, yana da yaÆinin cewa yana biye da jagora kaifi Éaya. Addininsa, wanda shi ne jigon rayuwarsa, yana Æarfafar wannan jajircewa. Tsoron Ubangijinsa na bayyana a aikace, ba a baki kawai ba.
Lokacin da ya bar aikin gwamnati a ranar 30 ga Mayu, 2025, ya yi hakan a sirrance. Ba hayaniya, babu sharholiya. Wannan wata alama ce ta tabbacin mutum da ya san aikinsa na Æwarai na wakiltarsa har a wuraren da Æafarsa ba ta taka ba. Tasirinsa bai tsaya ga muÆami ba. Tsarabar da ya Éauko ta Æwarewa ce, riÆo da gaskiya da kuma amana. WaÉannan abubuwa sun fi Æarfin kuÉi ya saya, sun kuma fi kowane mukami daraja.
Dole tattaunawar siyasa a Bauchi su canja salo. Jihar ta shallake matakin da za a yi ta maimaita dabaru da ayyukan baya da tunanin samun sabon sakamako. Æalubalen da muke fuskanta sun Æaru, mutane sun zaÆu don ganin kawo sauyi, damar yin kuskure a mulki ta Æara tsada. Wannan ba lokacin jin daÉi ba ne, lokaci ne na yanke shawara mai maâana. Dabarun siyasa kaÉai ba za su wadata ba, har da zurfin fahimta, ilimin tattalin arziki, da ikon juya buri zuwa sakamako.
A wannan gaÉar, yana da kyau mutanen Bauchi su tantance Bala Wunti, saboda yadda ya gudanar da rayuwarsa na alamta dacewarsa da angwancewa da jiharmu mai albarka. Yana da fahimtar tsarin mulki, ya gudanar da manyan ayyuka masu sarÆaÆiya cikin tsari da nasara. Yana da fahimtar jamaâa da ta samo asali daga yadda ya taso, ba hasashe kawai ba. Abu mafi muhimmanci, ba ya cikin rikice-rikicen siyasa da suka daÉe suna addabar jihar. Wannan nisa da ya yi da surkullen siyasar ya tsaftace shi daga zargi da Éatanci, haka kuma ya kare shi daga bayyana a matsayin wani Éangare na waccan daÉaÉÉiyar hauma-haumar siyasa, ana ma iya cewa ya zama wata hanya ta Éinke Éaraka da haÉa kawunan masu mabambanta raâayin siyasa.
Gabatar da shi a matsayin mafi dacewa da kujerar gwamnan Bauchi ba raâayi ne da na gabatar bisa son zuciya ba, duk da dai labarin rayuwarsa yana taÉa zuciyar. Dalilin ganin dacewar sa yana da tushe mai wuyar Æaryatawa. Tushen sa shi ne Æwarewa, sanin makamar aiki, da tarihi da ke nuna sanin kai da jajircewa. A lokacin da amana ta yi Æaranci, shigar sa siyasa ta zama kamar saukar ruwan sama ne bayan fari. A inda rarrabuwa kai ke raunana alâumma, kasancewarsa a tsakiya na iya kawo sauÆi. A lokacin da ake buÆatar Æarfin Æwanji, hangen nesa da kuma tausasawa, muna iya cewa ma kamar an yi Bala Maijamaâa Wunti don ya zo a wannan lokacin ya ceci jiharmu ne.
Gabatar da shi a matsayin mafi dacewa ba ya nufin shi cikakke ne ko ya kore masa yiwuwar yin kuskure, duk Éanâadam ajizi ne, kuma cikar kamala na ga Ubangiji. Sannan shugabanci ba ya tsayawa a buri kaÉai, ana ganinsa a yadda mutum ya gina rayuwarsa. Idan ana batun Bala Wunti, waÉannan hujjoji suna nan a fili. Daga tasowar sa cikin Æalubale zuwa aiki mai matuÆar tasiri, muna iya cewa an riga an gwada shi, kuma an san na Æwarai ne.
Bauchi na gab da yin zaÉi mai nauyi da tasirinsa ya fi zarce sanannun sunaye ko fastar zawarawanta. ZaÉi ne tsakanin nanata tsoffin hanyoyi da dabaru, da kuma yin garambawul ga tsarin gudanarwa da kawo sauyin da zai inganta rayuwar alâumma, zaÉi ne tsakanin abin da aka saba da abin da ake matuÆar buÆata. Idan mutanen jihar na son samun makoma mai cike da kwanciyar hankali, Æwarewa, da ci gaba da zai karaÉe kowa da koâina, dole ne su gane wanda ya shirya samar da hakan idan sun gan shi.
Bala Wunti na da Æwarewa, kyawawan halaye, da sanin makamar aiki. Ba sai ya faÉi Æimarsa ba. Ayyukansa tabbatacciyar shaida ce ga nagatarsa. Tambayar ita ce: shin mutanen Bauchi sun shirya zaÉar irin mutumin da jihar ke matuÆar buÆata a wannan gaÉar?
Idan sun shirya, to amsar tana gabansu.
Usman Abdullahi Koli
me********@***il.com.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








