Skip to content
September 20, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Education

ASUP Ta Ba Gwamnatin Tarayya Wa’adin Kwanaki 21 Kan Bukatun Malamai Da Ba a Cika Ba

August 22, 2025 3 minutes read

By Muhammad Sani Muazu

Kungiyar Malaman Kwalejojin Kimiyya Fasaha a Najeriya (ASUP) ta bai wa Gwamnatin Tarayya wa’adin kwanaki 21 domin warware muhimman matsalolin da ta ce suna barazana ga makomar ilimin kwalejojin kimiyya da fasaha a ƙasar nan.

Shugaban kungiyar na shiyyar B, Lumpye Innocent Simji ne, ya bayyana hakan a taron manema labarai da kungiyar ta gudanar a Bauchi a ranar Juma’a, inda ya ce an yanke wannan shawarar ne bayan taron gaggawa na majalisar zartarwar ƙasa ta kungiyar (NEC) da aka gudanar a Abuja a ranar 14 ga watan Agusta, na shekarar 2025. Ya yi gargadin cewa idan gwamnati ta yi biris, kungiyar ba za ta yi wata-wata ba wajen shiga yajin aiki a fadin kasar nan.

Daga cikin matsalolin da ASUP ta lissafa har da rashin sakin takardar umarni daga Hukumar Albashi ta Kasa (NSIWC) domin biyan “alawus alawus din karantarwa”, rashin biyan bashin karin albashin kashi 25/35 cikin 100, da kuma gazawar wasu gwamnatocin jihohi wajen aiwatar da sabon tsarin albashi da mafi ƙarancin albashi na kasa.

Sauran bukatun sun haɗa da jinkirin amincewa da tsarin da zai kawar da wariyar da ake yi tsakanin masu digiri da masu takardar HND, rashin sakin kudaden tallafi na NEEDS Assessment da aka amince da su don ci gaban gine-gine, matsalar kwace aikin tabbatar da inganci daga hukumar NBTE zuwa hannun masu zaman kansu da ba su cancanta ba, da kuma rashin kafa hukumar da za ta kula da bangaren kwalejojin kimiyya da fasaha kai tsaye.

Kungiyar ta kuma yi korafi kan jinkirin biyan kudaden karin matsayi na malamai tun daga shekarar 2019, rashin kammala tattaunawar sabunta yarjejeniyar kungiyar ASUP da gwamnatin tarayya na shekarar 2010, da kuma kin aiwatar da wasu sassa na dokar kwalejojin kimiyya da fasaha ta Tarayya a cikin kwalejojin jihohi. Haka kuma ta koka kan ci gaba da wariyar da ake yi wa masu HND a cikin aikin gwamnati da kuma rashin kammala tattaunawa kan biyan bashin matakin albashi na CONTISS 15.

ASUP ta yi tir da abin da ta kira karfi a harabar Kwalejin kimiyya da Fasaha ta Tarayya, da ke Nekede, inda ake zargin ana tura jami’an tsaro dauke da makamai domin hana ayyukan kungiyar. Kungiyar ta zargi Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da rashin daukar mataki kan wannan lamarin.

Simji ya ce rashin son tattaunawa da gaskiya daga bangaren Ma’aikatar Ilimi ya bar kungiyar da zabi guda – na bayar da wa’adin kwanaki 21. Ya gargadi cewa idan ba a dauki matakin gaggawa ba, ASUP za ta shiga yajin aiki tare da dakatar da dukkanin ayyukan koyarwa a kwalejojin kimiyya da fasaha na gwamnati a fadin kasa.

Tags: Academic Staff Union of Polytechnics (ASUP) federal ministry of Education National Board for Technical Education NBTE President Bola Ahmed Tinubu

Post navigation

Previous: INEC Urges Bauchi Voters to Register, Correct Records, and Replace Lost PVCs
Next: YLN, Partners Collaborate to Develop Bauchi State Policy on Gender in Education

Related Stories

  • Education

ASUU Bauchi Zone Decries Non-Implementation of 2025 FG Agreement

May 22, 2026
  • Education

CODE Programme Boosts Girls’ Skills, Sparks Call for Curriculum Reform in Bauchi

April 1, 2026
  • Education

SAZU Set for Combined Convocation, 11,813 Students to Graduate

March 28, 2026

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.