Skip to content
September 14, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Ƴan bindiga na cin karesu ba babbaka a Katsina

October 28, 2023 3 minutes read

Jama’a a ƙaramar hukumar Faskari ta jihar Katsina sun ce sun shiga tsaka mai wuya sakamakon yadda ‘yan bindiga suka mamaye garuruwansu, kuma suka mayar da su tamkar bayi.

Mazauna yankin sun ce ƴan bindigar sun kwace gonakin jama’a, tare da tilasta wa mutanen garuruwan yi masu shuka da huɗa da ma sauran ayyukan gona.

Yanzu haka dai jama’ar da ƴan bindigar suka mamaye a yankin ƙaramar hukumar Faskarin ta Najeriya suna cikin ƙunci da damuwa.

Wani mazaunin yankin da ya nemi a sakaya sunan sa ya shaidawa BBC cewa ƴan bindigar suna shiga ƙauyuka kuma su yi abin da suke so, kuma a lokacin da suke so.

Ya ce ‘‘A yanzu maganar da ake a cikin firamare din Kogo ƴan bindiga ne a ciki zaune, in an yi abinci a kai masu, in suka ga yarinya su ɗauka, in kuma ka yi magana su kashe ka.’’

Mutumin ya ce mazauna yankin suna biyayya ne ga ƴan bindigar saboda basu da wani zaɓi na daban.

‘‘tashin farko dai suka sa aka haɗa masu kuɗi cikin yarjejeniyar da aka yi, da kuma gonakin da suka ware waɗanna ba za a noma ba, su za a nomawa. Duk lokacin noma za mu je can, mu yi masu hu mu yi masu noma, mu yi masu huɗa, su faɗa mana abin da za a noma, mu yi noma kuma idan lokacin girbi ya yi mu kwashe mu basu. Sun maida mu tamkar bayi a cikin wannan yanki, idan ka yi kaifi a hukunta ka’’.

Ya ce ƙauyukna yankin da suka haɗa da Birnin Kogo da Yar-tsamiya da Kahi da Fankama da Hayin Dungu da kuma Gobirawa duk ƙarƙashin ikon ƴan bindigar suke, waɗanda ke ci gaba da murgunawa jama’a.

Dr Nasir Mu’azu, kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jihar Katsina ya ce gwamnatin jihar ta farga da wannan lamari.

‘‘Mutane a irin waɗannan ƙauyuka sun je sansanin ƴan gudun hijira, to kuma wasu da yawa ba za su iya haƙuri da zaman sansanin ba don haka sai suka koma ƙauyukan su, suna ci gaba da zama bisa ga yadda ƴan bindigar suke ta gallaza masu’’

Dr Nasir ya ce gwamnan jihar Katsina Dikko Umar Radda yana aiki tuƙuru don kula da mutanen da matsalar tsaron ta tilasta masu yin hijira da kuma tabbatar da tsaro a faɗin jihar.

Gwamnatin jihar Katsina dai ta lashi takobin magance matsalar tsaro da ta dabaibaye garuruwa da ƙauyuka da dama na jihar. Kuma ko a kwanan nan sai da ta ƙaddamar da rundunar sintiri ta farar hula don taimakawa wajen tabbatar da tsaro.

BBC Hausa

Tags: 'Yan Bindiga Katsina

Post navigation

Previous: Sojoji sun kashe ƴan Boko Haram 6 a Yobe
Next: L-PRES National Team Visits Bauchi On A Technical Support Mission

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.