Skip to content
September 14, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025 3 minutes read

Daga Umar Sani Yakubu

Wani jigo na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Jihar Bauchi, Kwamared Sabo Muhammad, ya bayyana a ranar Laraba cewa jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP) ta rasa tsarin siyasa da shugabanci a jihar.

Yayin wani taron taya shi murna da kungiyar Shehu Buba Vanguard (SBU) ta shiry Sabo Muhammad ya ce duk da irin nuna karfi da PDP ke yi, APC za ta kwace mulki daga hannun jam’iyyar a zaben 2027 mai zuwa.

Ya danganta rashin tsari a PDP da rashin samun sahihin dan takara da zai iya gogayya da wadanda APC ke da su. A cewarsa, “PDP ta rasa shugabanci saboda rashin dan takara nagari da zai iya tsayawa kafada da kafada da ‘yan takararmu.”

Jigon na APC ya jaddada muhimmancin hadin kai da jituwa a cikin jam’iyyar APC, yana mai cewa jam’iyyar na da dan takara nagari wanda ya san halin da jihar ke ciki.

Ya bayyana yadda APC ke amfani da duk wata dama da shaidu da take da su domin tabbatar da nasara a zaben shekarar 2027.

Sabo Muhammad, wanda aka nada a matsayin mai taimakawa sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu kan sadarwa, ya ce an riga an tanadi tsari na yada labarai da zai tallata dan takarar jam’iyyar tare da samar da daidaito da hadin kai a harkar yakin neman zabe.

Ya jaddada bukatar hadin gwiwa da fahimta tsakanin ‘ya’yan jam’iyyar domin cimma burinsu.

A nasa bangaren, Darakta Janar na kungiyar Shehu Buba Vanguard, Ishaq Dabo, ya bayyana cewa taron na musamman ne domin taya Kwamared Sabo Muhammad murna bisa nadin sa a matsayin mai taimakawa Sanata Shehu Buba Umar kan harkokin yada labarai.

Haka kuma, ya bayyana aniyar Sanata Shehu Buba na tsayawa takarar gwamna a zaben shekarar 2027, yana mai cewa shi ne dan takarar da ya dace da jam’iyyar APC a jihar.

Ishaq ya ce irin tasirin da Sanatan ke da shi da ayyukan da ya gudanar ya tabbatar da cancantarsa da dacewarsa da wannan mukami.

A cewarsa: “Ya samar da ayyukan yi ga matasa, ya tallafa wa matasa da kayan sana’a. Ya gyara da kuma gina makarantun firamare da cibiyoyin kiwon lafiya. Kuma a karo na farko a Bauchi, ya kawo titin kwalta.”

Ya jaddada cewa Shehu Buba shi ne cikakken dan takara da za a iya tallatawa ga jama’ar jihar.

Wakilinmu ya tattaro cewa Shehu Buba Vanguard (SBU) kungiya ce da aka kafa domin tallafa wa burin Sanata Shehu Buba na tsayawa takarar gwamnan Jihar Bauchi a zaben 2027.

Tags: All Progressive Congress (APC) People's Democratic Party (PDP) Senator Shehu Buba Umar Shehu Buba Vanguard (SBU)

Post navigation

Previous: Matasa da ‘Yan Majalisa Sun Tattauna a Bauchi Don Kara Karfafa Dimokuradiyyar Shigo da Jama’a
Next: Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

Matasa da ‘Yan Majalisa Sun Tattauna a Bauchi Don Kara Karfafa Dimokuradiyyar Shigo da Jama’a

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.