Wata ƙungiya mai zaman kanta, mai suna Accountability and Democratic Project (ADEP) ta rubutawa shugaban Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta ta Ƙasa, INEC da ya cire sunan tsohon babban hafsan sojojin sama na ƙasa, Abubakar Saddique daga yi wa jam’iyar APC takara a jihar Bauchi.
Kungiyar ta nuna bukatar neman cire sunan Sadique a matsayin ɗan takara na cikin wata takarda da rubuta ta kuma aike wa INEC.
Kungiyar ta yi koken cewa dan takarar bai gabatar da cikakkun takardunsa ga hukumar zaben, kamar yadda doka ta tanada ba.
A cewar kungiyar, Air Marshall Abubakar bai sanya wasu muhimman takardunsa waɗanda za su tabbatar da bayanan da ya cike a form din INEC mai suna EC 9 ba.
Abubakar Sadique a ya riƙe muƙamin babban hafsan sojan sama kafin ritayarsa da kuma shiga siyasa.
Ya zama ɗan takarar jam’iyyar APC a Bauchin ne bayan ayyana shi a matsayin wanda ya lashe zaben fidda-gwani wanda aka gabatar a cikin watan Mayu.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.