Skip to content
September 20, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

An kama wasu mutum uku kan Sace Tirela Mai Dauke Da Kayan Miliyan 550

October 14, 2023 2 minutes read

 

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Oyo ta bajekolin wasu mutum uku da ta ce an kama su ne da zargin karkatar da akalar wata tirela da ke makare da bandir-bandir na shimfidun kafet a Jihar.

A cewar rundunar, darajar kayan ta kai kimanin Naira miliyan 550.

Kakakin Rundunar, Mista Olawale Osifeso, ya ce wadanda ake zargin, masu suna Moses Olatunji da Lawal Adesina da Teslim Olapade, an kama su ne a maboyarsu da ke kan titin Ring Road a Ibadan, babban birnin Jihar.

Ya ce a lokacin da aka kama su, an yi nasarar gano wannan kaya da kuma motar tirelar da suka yi amfani da bindiga wajen tilasta wa direbanta karkatar da akalarta zuwa maboyar tasu.

Jagoran wadannan barayi, Moses Olatunji, bai musanta laifin da ake zargin su da aikatawa ba.

Ya shaida wa ’yan jarida cewa wannan ba shi ne kame na farko da aka yi masa ba.

Moses ya ce an sha kama shi a kan irin wannan laifi da yake yi a kan babbar hanyar Ibadan zuwa Legas.

Su ma Lawal Adesina da Teslim Olapade ba su bata lokaci ba wajen fadin irin rawar da suka taka a aika-aikar.

Mutum ukun dai na cikin guda 31 da rundunar ta yi bajekolin nasu. Sauran wadanda ake tuhumar kuma an same su da kayayyakin da suka hada motoci da babura da makamai, kuma ana zarginsu da aikata fashi da makami da garkuwa da mutane a sassa daban-daban na Jihar ta Oyo.

Jaridar Aminiya

Tags: Oyo Ƴan sanda

Post navigation

Previous: Wike Ya Yi Wankin Babban Bargo Wa EU Kan Zaben 2023
Next: WCS Trains Security Rangers To Protect Wildlife In Yankari 

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.