Skip to content
September 13, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Al’ummar Gari Sun Kashe ƴan Ta’adda 21 A Kebbi

September 22, 2023 2 minutes read

 

Yan bindiga 21 sun sheka lahira bayan jama’ar gari da ’yan banga sun yi musu kwanton ɓauna a yankin Danko Wasagu na Jiajr Kebbi.

Shugaban Ƙaramar Hukumar Danko Wasagu, Hussaini Aliyu-Bena, ya ce ’yan bindigar na tsallakowa zuwa Jihar Kebbi daga yankin Mariga na Jihar Neja ne, ’yan banga da jami’an tsaro suka yi musu kwanton ɓauna a Tudun Bichi suka kashe 21 daga cikinsu.

Ya bayyana cewa ƙaramar hukumarsa ta yi iyaka da yankin Mariga, shi ya sa ’yan ta’addan suke samun sauƙin tsallakowa zuwa Jihar Kebbi ta nan.

Ya ce ’yan bindiga sun kashe Marafan Mai Inuwa da ke yankin Kanya, suka yi garkuwa da wasu mutane, amma daga baya sojoji sun ƙwato mutanen.

Ya roƙi gwamnati ta girke ƙarin sojoji a yankunan Malekachi da Dankade, inda ’yan bindiga suke bi su wuce.

Sannan ya yaba da ƙoƙarin jami’an tsaro da ’yan banga da sauran mazauna yankin wajen daƙile ayyukan ’yan bindiga.

Shugaban Karamar Hukumar ya ce Gwamna Nasiru Idris ya ba da umarni a ziyarci al’ummar ƙauyukan da suka yi gudun hijira zuwa yankin Kanya a jajanta musu.

Aminiya ta nemi samun ƙarin bayani daga kakakin ’yan sandan jihar, SP Nafiu Abubakar, amma ya shaida wa wakilinmu cewa bai samu rahoto ba tukuna.

Jaridar Aminiya

Tags: Kebbi yan ta'adda

Post navigation

Previous: Tinubu Ya Maido Da Tallafin Mai, Ya Biya N169bn A Agusta
Next: Gwamnatin Tinubu na shirin tsara ƴan Najeriya da farfaganda – Atiku

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.