Wata kotu a Myanmar ta sake yankewa tsohuwar shugabar kasar Aung San Suu Kyi, daurin shekaru shida a gidan yari bisa samunta da laifin cin hanci, wanda hakan ke nuna cewar za ta kwashe jimullar shekaru 17 a gidan yari, kamar yadda wata majiya mai tushe da da ta nemi a sakaya sunanta ta sanar.
A lokacin zaman kotun, majiyar ta ce Aung San suu Kyi ta bayyana a cikin yanayi na koshin lafiya kuma ba ta yi wata magana ba bayan yanke hukuncin.
Suu Kyi, mai shekaru 77, ta na tsare tun bayan hambarar da gwamnatinta a ranar 1 ga Fabrairun bara, inda ake tuhumar ta da laifukan karya dokokin sirri na kasar da cin hanci da rashawa da kuma magudin zabe.
Kasashen duniya dai sun yi tir da wannan hukunci, ciki har da Amurka wacce ta ce wannan hukunci na baya-bayan nan rashin adalci da bin doka.
Shima babban jami’in kula da harkokin wajen kungiyar Tarayyar Turai Josep Borrel ya bayyana hukuncin da rashin adalci tare da yin kira da a gaggauta sakin ta.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.