Home News Gwamnatin jihar Bauchi da dakatar da kanyan sakatarorin gwamnati guda biyu

Gwamnatin jihar Bauchi da dakatar da kanyan sakatarorin gwamnati guda biyu

Hukumar kula da da’ar ma’aikata ta jihar Bauchi da dakatar da manyan sakatarori guda biyu, Sa’idu Abubakar da Danjuma Garba da kuma wani babban jami’i a bangaren kudi Bala Ibrahim bisa zargin saba ka’idar aiki.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na hukumar Saleh Umar, tana mai cewa dakatarwar ta fara aiki ne a ranar 27 ga watan Satumba na shekarar 2024 domin bada damar ci gaba da yin bincike.

Shugaban hukumar Alhaji Abubakar Usman ya gargadi ma’aikatan gwamnati da su kasance masu bin doka da oda, yana mai jaddada himmatuwar hukumar wajen tsaftace aikin gwamnati a jiha.

Jami’an da aka dakatar suna aiki ne a ofishin sakataren gwamnatin jiha, ma’aikatar ilimi mai zurfi da ma’aikatar ma’adinai.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.