Skip to content
September 14, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Matasa da ‘Yan Majalisa Sun Tattauna a Bauchi Don Kara Karfafa Dimokuradiyyar Shigo da Jama’a

July 30, 2025 4 minutes read

By Muhammad Sani Muazu

A wani yunƙuri na karfafa dangantaka tsakanin wakilan jama’a da matasa, kungiyar Young Leaders Network (YLN) ta shirya taron tattaunawa na State Legislative Pally a Bauchi, inda sama da wakilai 70 na ƙungiyoyin matasa, shugabannin dalibai da wakilan ƙungiyoyin fararen hula suka samu damar tattaunawa kai tsaye da ‘yan majalisar dokoki kan matsalolin da ke shafar matasa da al’ummomi.

Taron, wanda ya gudana a ƙarƙashin taken “Karfafa Dimokuradiyyar damawa da Jama’a a Matakin Jiha da Kananan Hukumomi,” yana daga cikin ayyukan zauren Citizens-Legislators Forum da kungiyar YLN ke gudanarwa a ƙananan hukumomi tara na Jihar Bauchi don karfafa sha’anin shugabanci nagari da tsoma bakin matasa cikin harkokin gwamnati.

An karanta sakon fatan alkhairi daga majalisar dokoki ta jihar Bauchi ta Mataimakin Kakakin Majalisar kuma shugaban kwamitocin majalisa na Matasa da Wasanni, Kasafin Kuɗi, da Tsaro. wanda ya yaba da kokarin Young Leaders Network wajen inganta hulɗar matasa da wakilan jama’a.

“Wannan taro ba kawai abu ne mai kyau ba, har ila yau yana nuna irin yadda matasa suka fara fahimtar muhimmancin tafiyar da gwamnati tare da jama’a,” in ji sakon. “Za mu ci gaba da maraba da haɗin gwiwa da ƙungiyoyi kamar YLN don inganta dimokuradiyya da walwalar jama’a.”

Rt. Hon. Mohammed Idris Musa, Kakakin Majalisar matasan Jihar Bauchi, ya halarci taron inda ya yabawa hangen nesa da basirar matasan da suka halarta.

“Matasanmu su guji zama a gefe. Su rika shiga irin waɗannan tarurruka masu amfani domin kara basira da bayar da gudummawa wajen gina al’umma,” in ji shi. “Dole wakilai su rage girman kai, su saurari jama’a yadda ya kamata.”

Ya ce kalaman da ke cewa gwamnati bata saurari jama’a ba sau da yawa suna da nasaba da son zuciya, inda ya nuna cewar gwamnatin yanzu ta ba matasa da mata dama a wurare masu mahimmanci.

Moses Danjuma Kusko, Manajan Ayyuka kan Matasa da shugabaci a kungiyar Young Leaders Network, ya ce taron ya samo asali ne daga tarukan tattaunawa da suka fara a matakin ƙananan hukumomi, inda yanzu ya kai matakin jiha.

“Mun yanke shawarar kawo matasa su yi magana kai tsaye da ‘yan majalisa, su fadi abubuwan da ke damunsu. Mun gayyato Shugaban Majalisa da shugabannin kwamitoci na Matasa, Kasafi da Tsaro domin su saurara da kansu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa za a fitar da takaitaccen bayani daga taron wanda zai ƙunshi mahimman batutuwa guda huɗu:

Shigar Matasan Cikin Mulki da Samar da Aiki

Ilimi da Tsabtace Muhalli (WASH)

Karfin Matasa da Gwamnati Mai Inganci

Shiga Harkokin Jama’a da Cigaban Al’umma

An kuma jaddada amfani da tsarin Community Charter of Demand – wani tsari da aka kirkira a Bauchi domin baiwa jama’a damar fitar da bukatun ci gaban su daga tushe.

Wadanda suka halarta sun nuna cewa za su yada ilimin da suka samu a cikin al’ummominsu. Maryam Musa, wata mai rajin kare hakkin mata da matasa, ta bayyana taron a matsayin ci gaba mai ma’ana.

“Yawancin jama’a basu san cewa ci gaba yana farawa daga gare su ba. Na fahimci cewa sai mun farka mun matsa lamba kafin gwamnati ta motsa. Zan koma gida in zama jakadiyar wannan shiri domin wayar da kan mutane,” in ji ta.

Taron ya hada matasa, kungiyoyin fararen hula na matasa da mata, shugabannin dalibai da masu ruwa da tsaki na al’umma domin tattaunawa cikin gaskiya da neman mafita. YLN ta ce tana fatan shigar da irin wannan tsarin a matsayin al’ada a harkar dokoki a jihar Bauchi.

Yayin da taron ya kare, mahalarta da jami’an gwamnati sun bayyana fatan cewa muryoyin da aka ji a taron za su zama ginshikin kudurori da dokokin da za su wakilci muradun matasa da jama’ar jihar baki daya.

Tags: Bauchi State House of Assembly National Endowment for Democracy Young Leaders Network

Post navigation

Previous: Foundation plants trees in Bauchi communities to combat desertification, climate change
Next: “Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.