Home News Kasar Rasha Za Ta Taimaka Wa Najeriya A Yaki Da Ta’addanci

Kasar Rasha Za Ta Taimaka Wa Najeriya A Yaki Da Ta’addanci

Shugaban Kasar Rasha, Vladimir Putin ya yi alkawarin taimaka wa Najeriya wajen yakar ta’addanci da kuma masu tsattsauran ra’ayin addini.

Shi dai Putin ya bayyana hakanne a lokacin da ya karbi bakuncin jakadar Najeriya a kasar farfesa Abdullahi Y. Shehu wanda ya mika takardar kama aiki a fadar Krelim.

Putin, ya kuma jadadda aniyarsa ta ci gaba da yaki da ta’addanci a fadin duniya, inda yace kasarsa za ta martaba duk wata kasa da take da alaka da ita wajen tallafa mata ta fuskar sha’anin tsaro, don karfafa alakar da ke tsakaninsu.

Kazalika, shugaba Putin ya yi karin haske kan yadda annobar cutar COVID-19 ta kawo tsaiko a fadin duniya, tare da cewar kasar shi ta kammala samar da rigakafin allurar cutar wadda za’a yi amfani da shi wajen dakile cutar.

Shugaban, ya kuma bayyana aniyarsa ta kulla yarjejeniya da kowace kasa da ke shirin amsar rigakafin cutar COVID-19 da kasar shi ta samar.

A nasa jawabin, sabon Jakadan na Najeriya a kasar Rasha, nuna jin dadinsa yayi bisa irin alakar da ke tsakanin kasashen biyu wago Najeriya da Rasha, yana mai isar da sakon gaisuwar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ga Shugaban na kasar Rasha.


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.