Skip to content
September 21, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Kungiyar Miyetti Allah Ta Gargadi Manoma Kan Yin Noma akan Duwatsu da Gefen Hanya Don Kaucewa Rikici a Bauchi

July 7, 2025 3 minutes read

Shugaban Miyetti Allah Kautal Hore reshen jihar Bauchi, Alhaji Muhammad Hussaini, ya gargadi manoma a jihar da su guji yin noma a akan duwasu da kuma gefen hanyoyi domin kaucewa rikicin manoma da makiyaya.

Alhaji Hussaini ya bayyana hakan ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a Bauchi, bayan kafa kwamitin da gwamnan jihar ya yi domin samar da mafita ta dindindin kan rikicin manoma da makiyaya a jihar.

Ya bayyana cewa kan duwatsu ne kadai wuraren da suka rage domin makiyaya su ciyar da dabbobinsu, inda ya roki manoma da su guji yin noma a irin wadannan wurare domin kaucewa rikici.

“Mun sha gargadin makiyaya da su kiyaye dabbobinsu, amma yadda makiyaya ke dawowa Bauchi da yawa, ba za mu iya ci gaba da wannan tsarin ba,” in ji shi.

Ya kara da cewa kwamitin da ya kunshi Kwamishinan ‘yan sanda, Daraktan Hukumar DSS da sauran jami’an tsaro, inda ya bayyana a fili cewa ba a yarda a yi noma a gefen hanya ko akan duwatsu ba, yana mai gargadin cewa duk manomin da ya karya wannan yarjejeniya, idan aka masa barna, kar ya zargi kowa, ya zargi kansa.

“Manoma su daina yin noma a gefen hanyoyi, musamman tsakanin mita 30 daga hanya, domin hakan ya saba da yarjejeniyar da aka cimma. Idan manoma sun yi noma a irin wadannan wurare kuma dabbobi sun ci amfanin gona, bai kamata su yi kuka ba,” in ji shi.

Sai dai Alhaji Hussaini ya jaddada cewa idan makiyaya sun bar dabbobinsu suna kiwo a gonakin mutane da ke wajen wadannan wuraren da aka hana, za a dauki mataki a kansu kan duk wani barnar da aka yi.

Ya kuma yi kira ga shugabannin gargajiya na Fulani da su ja kunnen mambobinsu kan muhimmancin bin doka, yana mai cewa kungiyar Miyetti Allah ba za ta goyi bayan duk wani dan kungiyar da aka samu yana karya doka ba.

“Ina kira ga ‘yan uwa Fulani da su zama masu bin doka, kuma ba za mu taba goyon bayan duk wani mai karya doka daga cikin mambobinmu ba,” in ji shi.

Alhaji Hussaini ya kuma roki manoma da su mutunta hakkin makiyaya tare da bin yarjejeniyar da aka tsara domin samun zaman lafiya mai dorewa a tsakanin al’umma.

Ya nuna damuwa cewa idan manoma da makiyaya suka kasa mutunta wannan doka, yawan dabbobin da ke dawowa Bauchi ka iya janyo rikici a jihar idan ba a dauki matakan gaggawa ba.

Tools

Tags: Bauchi Miyetti Allah Bauchi State Government Department of State Service Governor Bala Abdulkadir Mohammed Nigeria Police Force

Post navigation

Previous: Bauchi First Lady’s Humanitarian Gesture Empowers Vulnerable Residents
Next: Miyetti Allah Warns Farmers Against Cultivating Rocky, Roadside Areas to Avert Crisis in Bauchi

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.