Latest:
Labarai

Mun nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jami’anta suke jagoranta a Zamfara – Dauda

 

Gwamna Dauda Lawal, ya mayar da martani ga Ministan Labarai, Mohammed Malagi kan batun sulhun da ake yi cikin sirri da ‘yan bindiga.

Ya ce Gwamnatin Zamfara tana da gamsassun hujjoji da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya da hannu dumu-dumu a shirya zaman sulhu da ‘yan bindiga.

A jiya ne Ministan na Labarai da Wayar da Kai, Alhaji Mohammed Malagi ya zargi Gwamnatin Zamfara da siyasantar da lamarin tsaro. Biyo bayan neman ƙarin bayani da Gwamna Dauda ya yi kan zargin zaman sulhu ta ƙarƙashin ƙasa da ‘yan bindiga.

A wata takardar manema labarai, mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya bayyana cewa Gwamnatin Dauda Lawal tana da hujjoji masu tayar da hankali da ke fallasa wasu jami’an Gwamnatin Tarayya kan sulhu da ‘yan bindiga.

Ya ƙara da cewa Ministan na Labarai ya yi ri-ga mallam masallaci wurin yanke hukunci tare da yankewa gwamnatin Zamfara hanzari.

Sanarwar ta ci gaba da cewa: “Mun nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin Tarayya kan zaman sirri na sulhu da wasu jami’anta suke jagoranta a Zamfara ba tare da sanin Gwamnatin Jiha ko shugabanni jami’an tsaron jihar ba.

“Muna da gamsassun hujjoji dake tabbatar da wannan zaman sulhu tsakanin jami’an Gwamnatin Tarayya da ‘yan bindiga a wurare mabambanta a Zamfara.

“Akwai ban takaici a ce Ministan Yaɗa Labarai zai fito bainar jama’a ya kore batun ba tare da ya nemi sani daga jami’an tsaro ko ‘yan uwanshi da ke da hannu dumu – dumu a lamarin ba. Mun tsammaci tunda ƙwararre ne a harka watsa labarai, zai bi matakan da ilimi ya sharɗanta don tabbatarwa ko kore batun namu.

“Gwamnatin Jihar Zamfara tana matuƙar mutunta ƙa’ida tare da ganin ƙimar hukuma. Ba za mu fito kafafen watsa labarai muna fallasa sunayen jami’an Gwamnatin Tarayyan da ke wannan ta’asa ba, amma mun sanar da ‘yan Nijeriya don su nemi ƙarin bayani daga Gwamnatin ta Tarayya.

“Muna so mu sanar da Minista cewa jami’ansu na Gwamnatin Tarayya da ke jagorantar wannan zaman sulhu da ‘yan bindiga, sune ke siyasantar da matsalar tsaro, ba Gwamnatin Zamfara ba.

“Ba mu san daga inda Ministan ya samu ƙwarin gwiwan bugun ƙirji ya ce babu wani zaman sulhu da aka yi a Zamfara ba, saboda ai mun bayyana wuraren da aka yi waɗannan zama, irinsu Birnin Magaji, Maradun, Mun Haye, Ajah, Bawo, da kuma Bagege.

“Muna sake nanatawa cewa sulhu da ‘yan bindiga a Zamfara ba zai taɓa haifar da ɗa mai ido ba. Sam! Ba wannan ba ne mafita ga matsalar, a yi amfani da qarfi kawai a kauda su, wanna ita ce matsayarmu har gobe.

“Muna kira ga Gwamnatin Tarayya da ta daina biye wa ‘yan amshin Shata, ta yi bincike tare da wanke kanta daga aikin waɗannan dillalan sulhu da ‘yan bindiga.” In ji shi.

Jaridar Leadership