Home National News Shugaba Buhari Ya Nada Sababbin Ministoci

Shugaba Buhari Ya Nada Sababbin Ministoci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada sababbin ministoci bakwai domin maye gurbin wadanda suka sauka da wadanda ya sauke daga kan mukamansu.

Shugaban majalisar dattawa Sanata Ahmed Lawan ne ya karanto sunayen sababbin ministocin da Shugaba Buhari ya aike wa majalisar a zaman da ta yi ranar Talata.

Sabbin ministocin sun hada da Ibrahim El-Yakub daga Jihar Kano, Umana Okon Umana daga Akwa Ibom, Henry Ikechukwu Iko daga jihar Abia, Ademola Adegoroye daga jihar Ondo, sai Odum Odi daga jihar Rivers.

Sauran su hada da Goodluck Nnana Opia daga jihar Imo da kuma Joseph Ukama daga Ebonyi .


Discover more from Albarka Radio

Subscribe to get the latest posts sent to your email.