Skip to content
September 20, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Security

Yan Sanda Sun Kama Masu Satar Shanu, Sun kuma Kwato Shanu guda 10 a Bauchi

August 23, 2025 2 minutes read

Daga Zainab Kasim Ibrahim

Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu da ake zargi da satar shanu guda biyu inda ta gano shanu 10 da aka sace a kauyen Maikwangi,na karamar hukumar Ningi.

Wadanda aka kama sun hada da Umar Usman, mai shekaru 24, da kuma Auwal Mohammed, mai shekaru 22, daga karamar hukumar Sabo, a Jihar Kaduna. An kama su ne a ranar 14 ga watan Agusta, 2025, bayan samun bayanan sirri.

Bisa ga sanarwar rundunar, jami’an ‘yan sanda daga ofishin‘yan sanda na Ningi tare da hadin gwiwar jami’an tsaro na wasu hukumomi, karkashin jagorancin DPO na Ningi, sun gudanar da samame har suka samu nasarar kama mutanen biyu.

A yayin da ake tuhumarsu, wadanda ake zargin sun amsa laifinsu inda suka bayyana cewa sun sace shanun ne daga wani makiyayi da ke dajin Gwamnare, a kauyen Maikwangi, kimanin wata daya da ya wuce.

Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da kama mutanen, inda ya nemi al’ummar Gwamnare da daukacin jama’a da su yada wannan bayani domin a gano ainihin masu shanun da aka sace.

Ya kara da cewa bincike na ci gaba, kuma daga bisani za a gurfanar da su a kotu.

Tags: Bauchi State Government Bauchi state police command Miyetti Allah Cattle Breeders Association Miyetti Allah Kautal Hore

Post navigation

Previous: Yan sanda sun cafke matasa biyu da ake zargi da sace wayoyin lantarki a Bauchi
Next: Police Arrest Suspects for Vandalizing and Stealing Electric Cables in Bauchi

Related Stories

  • Security

PCRC Warns Bauchi, Gombe Communities Against Harbouring Criminals

May 14, 2026
  • Security

NSCDC in Bauchi Arrest Man for making 7 Million naira Fake Bank Transfer for Car Purchase

March 6, 2026
  • Security

NSCDC Bauchi State Command deploys 1,100 personnel for Yuletide security

December 23, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.