Labarai

Ƴan Fashin Daji Sun Sace Kawayen Amarya A Katsina

Yan fashin daji sun afka garin Sukola da ke karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina inda suka yi awon gaba da mutane 6 ciki har da kawayen Amarya 5.

Jaridar katsina post ta rahoto cewa, wani mazaunin garin Sukola da ya nemi a sakaya sunan sa ne ya bayyana hakan.

Majiyar ta bayyana cewa, wadanda lamarin ya rutsa da su ba mazauna garin ba ne, makwabtan garin ne da suka zo don gudanar da shagulgulan bikin Amarya.

‘Yan matan sun hada da Maryam Sani, Maijidda Kabir, Abida Matthew da Maryam Ibrahim sai ta karshen wacce majiyar ta ce, sunan ta ya shige mata.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Katsina, ASP Sadiq Abubakar, ya tabbatar da afkuwar lamarin inda yace, jami’ansu na ci gaba da bincike kan ganin an kubutar da su cikin koshin lafiya.

Jaridar Leadership