Labarai

Shugaban karamar hukumar Lokoja ya rasu

 

Allah Ya yi wa Shugaban Karamar Hukumar Lokoja, Honarabul Muhammed Danasabe Muhammed rasuwa a Jihar Kogi.

Aminiya ta ruwaito cewa an tabbatar da rasuwarsa da misalin karfe 4:30 na Asubahin wannan Juma’ar a wani asibiti a Lokoja, babban birnin jihar.

Bayanai sun ce an garzaya da marigayin zuwa asibiti ne bayan ya yanke jiki ya fadi a gidansa.

Wakilinmu ya ruwaito cewa, Danasabe na daya daga cikin ’yan siyasar da ke sahun gaba-gaba wajen halartar taruka a shirye-shiryen zaben gwamnan jihar da za a yi a gobe Asabar.

Wata majiya daga bangaren iyalansa ta ce an mika Danasabe Asibitin Shifa da ke Lokoja bayan ya yanke jiki ya fadi a gidansa cikin dare kafin wayerwar gari Juma’a.

Majiyar ta ce za a yi jana’izarasa bayan sallar Juma’a sannan a binne gawarsa a makabartar Unguwar Kura.

Ya rasu ya bar mahaifiyarsa, mata da kuma ’ya’ya.

Kawo yanzu dai masu makoki da alhini sun yi ta tururuwa a gidan mamacin domin jajanta wa iyalansa.

Jaridar Aminiya