Skip to content
September 14, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Tinubu Ya Ciwo Bashin Tiriliyan 1.6 Daga Bankin Duniya A Cikin Wata 4

September 25, 2023 2 minutes read

 

Kawo yanzu, jimillar bashin da gwamnatin Tinubu ta karbo daga Bankin Dunia a cikin wata hudu ya kai Dala biliyan 2.15, wato kimanin Naira tiriliyan 1.6.

Hakan na zuwa ne bayan — a karo na uku cikin wata hudu — Shugaba Tinubu ya ciyo karin bashin Naira biliyan 536 (Dala miliyan 700) daga Bankin da nufin bunkasa bangaren ilimin ’yan mata da kuma ba su tallafi a Najeriya.

“Bankin Duniya ya amince ya kara wa Najeriya bashin Dala miliyan 700 domin Bunkasa Ilimin ’yan mata da ba da tallafi, wanda zai mayar da hankali kan ilimin sakandare a wasu jihohi.

“Karin rancen zai bunkasa ayyukan da akeyi a wasu jihohi bakwai zuwa 11 domin kara yawan wadanda za su amfana, ciki har da yan matan da ba sa zuwa makaranta, wadanda aka aurar da kuma nakasassu,” in ji sanarwar Bankin Duniyar.

Karo na uku ke nan a cikin wata hudu da Gwamnatin Tinubu ta samu bashin Bankin Duniya tun bayan hawan Tinubu a ranar 29 ga watan Mayu.

Kawo yanzu, jimillar bashin da gwamnatin Tinubu ta karbo a cikin wata hudu ya kai Dala biliyan 2.15, wato kimanin Naira tiriliyan 1.6.

Da farko Tinubu ya ciwo bashin Dala miliyan 750 domin bunkasa bangaren wutar lantarki,

A karo na biyu ya samu rancen Naira biliyan 383 (Dala miliyan 500) domin tallafa wa mata.

Sai kuma bashin Naira biliyan 536 (Dala miliyan 700) da ya ciyo a yanzu na bunkasa ilimin ’yan mata da kuma ba su tallafi.

Ofishin Kula da Basuka na Najeriya (DM), ya sanar cewa zuwa karshen watan Yuni, yawan bashin da Bankin Duniya ke bin Najeriya ya kai Dala biliyan 14.5, kimanin Naira tiriliyan 11.

A ganinku wane irin tasiri basukan da ake karbowa daga Bankin Duniya da sauran hukumomin duniya za su yi ga ’yan Najeriya?

Wace hanya ya kamata a bi domin hana karkatar da kudaden?

Jaridar Aminiya
Tags: Bankin Duniya Najeriya Shugaba Bola Ahmed Tinubu

Post navigation

Previous: An tsinci jariri a cikin gona a Jigawa
Next: An kulle Masallacin Jumma’a kan rikicin limancin a Lagos

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.