Skip to content
September 14, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Sojojin sunyi kutse ofishin EFCC domin kwato ƴan uwansu

November 18, 2023 (Last updated: November 18, 2023) 2 minutes read

 

Hukumar da ke yaƙi da yi wa tattalin arzikin Najeriya zagon ƙasa ta EFCC ta bayyana takaicinta kan yadda ta ce wasu jami’an sojin saman ƙasar suka kutsa ofishinta da ke Kaduna domin ƙwato ‘yan uwansu da hukumar ta tare bisa zargin ‘karya dokar aikin tsaro’.

Cikin wata sanarwa da hukumar ta fitar, mai ɗauke da sa hannun jami’ain hulɗa da jama’a na hukumar, Dele Oyewale, ta ce a ranar Litinin 13 ga watan Nuwamba jami’an EFCC sun kama wasu mutum biyar da hukumar ke zargi da aikata laifukan da suka shafi zambar kuɗi ta intanet a unguwar Barnawa da ke birnin Kaduna

Hukumar ta ce ta kama mutanen ne ba tare da wani tashin hankali ba, daga nan ne kuma wasu mutum shida – da suka haɗar da sojoji huɗu da ɗaliban cibiyar fasahar aikin sojin sama biyu – waɗanda ke wurin a lokaci da aka kama waɗanda ake zargin, suka yi wa ofishin EFCC da ke Kaduna ƙawanya da nufin tilasta sakin mutanen.

”Daga nan ne kuma aka kama su tare da tsare su a ofishin hukumar, bisa zargin karya dokar aiki tsaro”, kamar yadda sanarwar ta yi bayani.

A yayin da ake tare da mutanen hukumar EFCC ta ce ta tuntuɓi rundunar sojin sama ta ƙasa inda hukumomin biyu ke tattanawa domin warware lamarin.

Dele Oyewale ya ce a ranar Juma’a wasu jami’an sojin sama sun dirar wa ofishin EFCCn da ke Kaduna a cikin shirin faɗa, don tilasta sakin abokan aikin nasu.

“Hukumar EFCC ta yi aiki cikin nutsuwa, inda ta ci gaba da tattaunawa da jagororin rundunar sojin saman, kuma daga ƙarshe aka cimma matsayar sakin sojojin bayan an ɗauki bayansu”, kamar yadda mai magana da yawun EFCCn ya bayyana.

BBC Hausa

Tags: EFCC Kaduna Sojojin

Post navigation

Previous: Rikici ya ɓarke tsakanin ƴan sanda da jami’an shige da fice  a Maiduguri 
Next: Ƴan Boko Haram sun kai hari wa tawagar gwamnan Yobe

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.