Skip to content
September 8, 2026
  • About Us
  • Contact Us
  • Personal Information Usage Disclosure
  • Privacy Policy
Albarka Radio

Albarka Radio

Official Website of Albarka Radio, Bauchi.

Primary Menu
  • Home
  • Breaking News
  • Education
  • Health
  • National News
  • Latest News
  • Politics
  • Sports
  • Featured
Light/Dark Button
Listen Live
  • Labarai

Anyi wa Fasto dukan kawo wuƙa kan satar Mazakuta

November 9, 2023 1 minute read

 

Jam’aa sun yi wa wani lakcara kuma fasto duka tare da neman yi masa tsirara kan zargin satar mazakula yankin Wurukum da ke garin Makurdi a Jihar Binuwai.

Dokta Emmanuel Aime, wanda malami ne a Kwalejin Kimiyya da Kere-kere ta Akawe Torkula da ke jihar, ya je yin wa’azi ne a safiyar Laraba a kusa wa wani banki inda wani ya yi kururuwa cewa an sace masa mazakuta.

Mutanen da suka ritsa shi, sun bayyana cewa fitowar Dokta Emmanuel daga cikin banki ke da wuya wani matashi ya yi ihu da zargin shi da sace masa mazakuta.

Nan take mutane suka far masa da duka suka yi masa jina-jina suka yayyaga kayansa, saura dan kamfai kafin sojoji da wasu jami’an tsaro suka yi suka kwace shi.

Wani shaida a wurin ya ce daga baya an binciki matashin da ya yi zargin an sace masa mazakuta, amma aka same shi lafiya, shi ne aka garzaya da shi ofishin ’yan sanda.

Mai magana da yawun ’yan sandan jihar, SP. Catherine Anene, ta tabbatar da faruwar lamarin, wanda ta bayyana takaicinta a kansa.
Jaridar Aminiya
Tags: Benuwai Fasto Satar Mazakuta

Post navigation

Previous: An kama malamin sakandare kan zargin fyade a Ogun 
Next: Wani ɗan haya ya yi fyaɗe wa ƴar Fasto ta dauki ciki

Related Stories

  • Labarai

Sakon Sakatare Janar Na MDD Na Murnar Fara Azumin Ramadan 2026

February 17, 2026
  • Labarai

Fiye da Mata 100 Sun Kammala Samun Horo Kan Fasahar Sadarwar Zamani a Bauchi Karkashin Shirin Renewed Hope Initiative

July 30, 2025
  • Labarai

“Jami’ar PDP ba ta da alkibla a jihar Bauchi” In ji wani jigo a jam’iyyar APC

July 30, 2025

You May Have Missed

  • News

Nigeria Moves to Unlock $1.2bn ECOWAS Trade Market, Urges Nigerian Businesses to Conquer West African Markets

September 5, 2026
  • Opinion

Nigeria Rejoins World Energy Council – Wunti Takes the Helm

August 8, 2026
  • News

Fathers’ Forum Sparks Change in Bauchi, Men Rally Behind Girls’ Education

June 8, 2026
  • News

Bauchi Mothers Drive Grassroots Push for Girls’ Education and Empowerment

June 8, 2026
  • Home
  • About Us
  • Contact Us
  • Privacy Policy
Copyright © 2026 Albarka Radio, All rights reserved. | ReviewNews by AF themes.