News

APC Ta Bukaci Ganawa Da Tinubu, Kashim, Sanatoci, Yan Majalisan Wakilai

Jagorancin jam’iya mai ci a kasa, APC ta gayyaci zababben shugaban kasa Asiwaju Bola Ahmed Tinubu da kuma mataimakin sa Sanata Kashim Shettima , zababbun sanatoci dakuma mambobin majalisar wakilai domin gudanar da wata muhimmiyar zama.

Wanan taron ya na zuwa ne gabanin rantsar da Asiwaju Bola tinubu wanda a aka zaba don maye gurbin shugaba Muhammadu Buhari a babban zabe da ya gudan ranar 25 ga watan Fabreru. Zababben shugana zai kama rantsuwar kama aiki  ranar 29 ga watan Mayu. Da ga bisani kuma za a rantsar da zababbun yan majalisu a watan Yuni don kama aiki.

Zaman za’a gudanar dashi ne cikin sirri a ranar Litinin din nan kuma zai gudana ne a fadar shugaban Kasa dake birnin Abuja , zai kuma samu halartan masu ruwa da tsaki a bangaren siyasa domin lalumo bakin zare.

Duk da cewa ba’a bayyana tsarin kokuma ajandar zaman ba , Ammah wata majiya daga sakatariyan jam’iyar ta bayyana cewa zaman za’ayi shi ne kan dokar kasa dakuma shirye shiryen dabaru dasuka shafi batun shiyyoyi na majalisar fadar shugaban kasa , kakakin majalisar wakilai da sauran manyan ofisoshi dake majalisar dokoki ta kasa.

Majiyan yace suna tsammanin cewa zaman nadaga cikin wasu manyan hanyoyi dakuma yunkurin Kaura cewa mai maita Juyin mulki da akatabayi wanda ya kawo Sanata Bukola Saraki dakuma Yakubu Dogara a matsayin shugaban majalisar kasa dakuma shugaban majalisar dattijai a shekaran 2015 .

Majiya ln yayi bayanin cewa, wadan da sukayi juyin mulkin wa fararen hula da suka kawo Saraki da Dogara a shekaran 2015 har yanzu suna kan cigaba da farautar jam’iyar.

Leave a Reply