Daga Aminu Harsanu Guyaba
Sarkin Yaƙin Dr. Bala Wunti, Wanda ya Assasa, BMW Project
A yau, mutane da dama na rayuwa ba tare da hangen nesa ko fata na samun gobe mai kyau ba. Sau da yawa, wannan ba zabinsu ba ne, sai dai hukuncin Allah Maɗaukaki. Amma a cikin wannan duniyar, akwai wasu mutane da suke zama haske ga rayuwar wasu, suna ba da fata a inda babu ita.
A jihar Bauchi, muna da irin wannan mutum: Dr. Bala Maijama’a Wunti. Kokarinsa wajen tallafawa masu rauni da marasa galihu cikin al’umma ba shi da kishiya. Ya kasance yana kai dauki ga wadanda al’umma ta yi watsi da su, musamman matasa da suke da basira da gogewa a kasuwanci amma ba su da damar ci gaba da ayyukansu saboda rashin tallafi.
Jinƙan Dr. Bala Wunti ba na neman suna ba ne ko siyasa, a’a, sadaukarwa ce ta gaskiya da ya ke yi cikin nutsuwa domin canza rayuwar mutane. Matasa da dama da suka kasance cikin duhu sun sami sabon fata ta hanyar taimakonsa. A lokacin da yawancin shugabanni ke mantawa da matasa, Dr. Wunti ya nuna cewa tallafawa matasa hanya ce mafi kyau ta cigaban al’umma.
Zan faɗi ba tare da wata shakka ba cewa Dr. Bala Wunti mutum ne ɗaya cikin dubu. Tausayi da sadaukarwarsa sun bambanta shi a cikin al’umma inda mutane da dama ke jin nauyin taimakon masu bukata. A yau a Bauchi, babu wanda ya kai shi wajen hidima ga al’umma da zuciya ɗaya.
Saboda wannan hidima tasa ta dindindin, muna ganin lokaci ya yi da Dr. Bala Wunti zai amsa wani babban kira. Muna ganin lokaci ya yi da ya kamata ya tsaya takarar shugabanci mafi girma a jihar Bauchi, domin ya shimfiɗa wannan tausayi, basira da shugabanci nagari zuwa ga kowa. Wannan kira ba saboda son zuciya muke yi ba, sai dai saboda hujjojin abubuwan da ya riga ya yi da kuma abin da ya ke iya yi.
Ko kafin a fara maganar takarar wani mukami, Dr. Wunti ya dade yana aiki tukuru domin jama’armu, yana nuna mana yadda shugabanci na gaskiya yake. Wannan ne yasa ni da sauran mutane da dama muke roƙonsa da ya yi la’akari da wannan alhakin. Insha Allah, muna da yakinin cewa zai amsa wannan kira, saboda mutanen da suka dogara kuma suka yi imani da shi.
A halin yanzu, ina roƙon jama’ar jihar Bauchi da su ci gaba da yi wa Dr. Bala Maijama’a Wunti addu’a. Allah ya ba shi ƙarfi da hikima domin shugabanci idan lokaci ya yi, kuma Allah ya ci gaba da kare shi da taimaka masa a yayin da yake hidimtawa al’umma.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









