Labarai

Kisan Anambra: Kiris Ya Rage Na Haukace

Mutumin da aka kashe wa matarsa mai ciki wata tara da kuma ƴa’ƴansa huɗu a jihar Anambra dake kudancin Najeriya, ya ce ya ji kamar ya haukace saboda tashin hankalin da ya shiga.

Wasu ƴan bindiga da ake zargin ƴan ƙungiyar IPOB ne suka kai hari tare da kashe mutum 12 da suka ƙunshi mace mai ciki wata tara mai suna Harira Jibril da ƴa’ƴanta huɗu.

Mijin matar kuma mahaifin ƴa’ƴan dukkanin mata da aka kashe a harin ya shaida wa kafar BBC cewa an kashe matarsa ne da ƴa’ƴansa a lokacin da suke kan hanyar dawo wa daga ziyarar da ta kai, tare da ƴaƴanta a yankin Orumba ta arewa a jihar Anambra.

“Na shiga tashin hankali matuka, saura kaɗan na haukace – kamar an saka ni cikin wuta, haka nake ji saboda zafin da nake ji,” in ji Jibril Ahmed mijin matar da aka kashe da kuma ƴa’ƴansa huɗu.

“Yanzu ina zan fara – yaya zan yi aure har na samu ƴaƴan da Allah ya ba ni waɗanda har sun yi nisa da karatu.”

“Yarana suna da basira amma ga shi yanzu irin ɓarnar da aka yi min, kawai na yi tawakalli ga Allah – Allah zai saka min,” in ji shi.

Ya ce yanzu yana koƙarin samun motar da za ta ɗauki gawar matarsa da gawarwakin ƴa’ƴansa ne zuwa jihar Adamawa.

A cewarsa – yana son a binne gawarsu a jihar sa ta Adamawa.

“An caje ni naira dubu 170 na daukar gawarsu zuwa jihar Adamawa sannan na biya naira dubu 30 a dakin ajiye gawa,” in ji Jibril Ahmed.

Ya ce a cikin satin nan matarsa za ta haihu amma aka kashe ta.

“Iyayen matata sun shiga tashin hankali kuma ina ƙoƙarin tafiya da gawarta domin a binne ta garin iyayenta.”

A cewar hukumar ‘yan sandan Najeriya yanzu haka sun kama ƴan bindigar da suka aikata kisan na mutum 12 da suka ƙunshi har da mace mai ciki da ƴa’ƴanta huɗu.

Ƴan sanda sun ce suna zargin ƴan ƙungiyar IPOB masu fafutukar ɓallewa daga Najeriya ne suka aikata hakan.

Tashin hankali na ƙara ƙaruwa a jihar Anambra musamman hare-haren ƴan bindiga da ake kai wa kusan a kullum.

Lamarin ya ƙara ƙamari ne a jihar biyo bayan hare-haren da ‘yan bindiga ke kai wa a kullum.

Ko a ƙarshen makon nan an fille kan wani ɗan majalisar jiha wanda aka tsinci kansa da gawarsa gefen hanya bayan an sace shi a ranar 15 ga watan Mayu.

Kashe-kashen musamman matar da aka kashe da ciki da kuma ƴa’ƴanta huɗu ya fusata ƴan Najeriya musamman a kafofin sada zumunta na intanet.

Leave a Reply