Wani lauya a jihar Kano, Barista Badamasi Sulaiman Gandu, ya yi barazanar maka Hukumar Hisbah ta jihar Kano a gaban kotu, matukar ta gaza dakatar da shahararren mawakin nan, Ado Isa Gwanja, daga fitar da wata sabuwar waka da ya yi mai taken “Asosa”.
A makon nan ne dai Gwanja ya saki somin-taɓin waƙar a kafafen sada zumunta, inda a ka gano shi yana bin wakar tare da sosa jikinsa cewa kaikayi ya kama shi.
Da ya ke zantawa da manema labarai a yau Laraba, Barista Gandu ya ce tuni ya aike da takardun gargaɗi na kwanaki uku ga hukumomin Hisbah da Hukumar Shari’a ta jihar Kano domin su gaggauta dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar wakar.
Barr. Gandu, wanda ya zargi mawakin da yin amfani da kalaman da basu daceba acikin waƙoƙinsa, ya nuna cewa barin irin waɗannan wakokin a cikin al’umma zai kawo cikas wajen tarbiyyar yara masu tasowa.
Lauyan ya ce, kamata ya yi gwamnatin jihar Kano ta ɗauki mawakin aiki a karkashin hukumar Hisbah domin yin amfani da hikimarsa wajen faɗakar da al’umma saɓanin yadda ya ke amfani da hikimar ta wata hanya daban.
A ƙarshe, lauyan ya jaddada barazanar maka hukumar Hisbah agaban kotu matukar ta haura kwana uku bata dakatar da mawakin daga fitar da sabuwar waƙar ba.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.