Latest:
Labarai

Dawo Da Sufurin Jirgin Kasa Abuja-Kaduna A Yanzu Rashin Tausayi Ne – Minista Sufuri

Gwamnatin Tarayya ta ce damuwa da halin da iyalan wadanda ’yan bindiga suka sace a jirgin kasan Kaduna zuwa Abuja ne ya sa har yanzu ba ta dawo da zirga-zirgar jirgin ba.

Ta ce ta yi watsi da batun sake ci gaba da zirga-zirgar jirgin ne saboda yin haka a yanzu alama ce ta rashin tausayi ga iyalan mutanen.

Ministan Sufuri, Mu’azu Sambo ne ya bayyana hakan a ranar Laraba yayin da yake amsa tambayoyi daga manema labaran Fadar Shugaban Kasa a karshen taron Majalisar Zartarwa ta Tarayya.

Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari ne dai ya jagoranci taron a fadarsa da ke Abuja.

A cewar Ministan, wasu muhimman batutuwa biyu ne suka janyo jinkirin dawo da zirga-zirgar da aka dakatar bayan harin da aka kai wa fasinjoji a watan Maris na 2022.

Batutuwan, a cewarsa sun hada da halin da iyalan wadanda aka yi garkuwa da su da har yanzu suke hannun maharan ke ciki da kuma bukatar a samu na’urorin sa ido a kan hanyoyin don kaucewa aukuwar harin a nan gaba.

Ya ce gwamnati na duba mafi kyawun hanyar sa ido gami da amincewa da ita wajen tsaro a cikin tsarin hadin gwiwa da jama’a.

Da aka tambaye shi game da takamaiman lokacin tabbatar da tsaron layukan jirgin da za a aiwatar da shirin, Sambo ya ce: “Idan na ba da lokaci, zan yi muku karya. Zai zama rashin tausayi don sake ci gaba da sufurin jirgin idan wasu iyalai suna kuka dare da rana saboda har yanzu iyalansu suna cikin daji.”

Ministan ya kuma ce gwamnati na sane da kashe kudade, amma ya kamata ta iya bayar da rahoton tabbataccen ci gaban da aka samu nan da wata guda.

Leave a Reply