Latest:
Labarai

Mutum 40 sun ɓata bayan kifewar Kwalekwale a Kebbi

 

Kimanin mutum 40 ne ake zullumin sun bace bayan wani hatsarin kwalekwale a yankin Karamar Hukumar Yauri a Jihar Kebbi.

Jaridar Aminiya ta gano cewa kwalekwalen ya yi hatsari ne yayin da yake dauke da kaya da fasinjoji kimanin 50 a kan Kogin Neja a ranar Litinin.

Shugaban Karamar Hukuumar Yauri, Alhaji Bala Mohammed, ya ce fasinjojin da kwalekwalen sun taso ne daga kauyen Kasabo a Karamar Hukumar Agura na Jihar Neja a hanyarsu ta zuwa Yauri inda suka yi hatsari.

Ya ce hatsarin kwalekwale ya auku ne sakamakon karfin igiyar ruwa, kuma mutum 10 ne aka yi nasarar cetowa zuwa lokacin da muka samu wannan rahoto.

Amma ya ce “ana cii gaba da aikin ceto” da fatan sauran ma za a same su da ransu.

Jaridar Aminiya