Daga Abdulaziz Garba
Rundunar âYan Sanda ta Jihar Bauchi ta cafke wani mutum mai suna Kabiru Bala, Éan shekara 31 da haihuwa, bisa zargin aikata laifuffukan sata da lalata kayan gwamnati a sassa daban-daban na jihar.
Wanda ake zargin, mazaunin Æaramar hukumar Darazo ne, an kama shi ne bayan wani korafi da wani mai suna Dr. Auwal Abdullahi daga jihar Gombe ya shigar. A cewar âyan sanda, Dr. Abdullahi ya ce a ranar 20 ga Yuli, 2025, da misalin Æarfe 8:30 na safe, ya ajiye motarsa kirar Peugeot 307 mai lamba ABJ-982NC a masaukin da ke otal din Al-Umma Village Lodge, inda ya kama Éaki.
Da safiyar washegari, ya tarar da cewa an fasa gilashin motar tare da sace kayayyaki masu muhimmanci ciki har da:
Tsabar kudi har Naira Miliyan Biyar (N5,000,000)
Kwamfutar tafi-da-gidank
Waya kirar Tecno Smart 17
Bayan samun rahoton ne, rundunar âyan sanda ta fara bincike cikin gaggawa ta hanyar amfani da fasahar zamani, wanda hakan ya kai ga kama Kabiru Bala. A lokacin da ake tuhumarsa, wanda ake zargin ya amsa laifin da ake tuhumarsa da shi, tare da bayyana yadda ya dade yana aikata laifin satar wayoyin lantarki a wurare kamar su Alkaleri, Ningi, Darazo (Kari da Lanzai), da cikin garin Bauchi.
Ya bayyana cewa yana siyar da wayoyin wutar da ya sace bisa nauyinsu, inda ake saya Naira dubu goma (N10,000) akan kowanne kilo. A baya, ya siyar da kilo shida (6kg) inda ya samu Naira dubu sittin (N60,000). Ya Æara da cewa ya dade yana aikata irin wannan laifi tsawon kusan shekaru bakwai, kuma an kama shi sau takwas, inda ya sha zuwa gidan gyaran hali.
An kuma gano wasu daga cikin kayayyakin da aka sace a hannunsa, waÉanda suka haÉa da kwamfutar tafi-da-gidanka da wayar Tecno Smart 17.
Kakakin rundunar âyan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, wanda ya tabbatar da kama wanda ake zargin a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata, ya ce Kwamishinan âYan Sanda na Jihar Bauchi, Sani-Omolori Aliyu, ya bayar da umarnin gurfanar da wanda ake zargin a kotu da zarar an kammala bincike.
Wakil ya Æara da cewa rundunar tana ci gaba da bincike tare da kokarin kama sauran abokan haÉin gwiwa da masu sayen kayan da ake sacewa.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









