World News

Sama Da Mutum Miliyan 10 Ne Suka Ziyarci Masallacin Annabi A Azumin Bana

Hukumomin kasar Saudiyya sun ce aƙalla masu ibada miliyan 14 ne suka ziyarci Masallacin Annabi tsira da amincin Allah ya tabbata gareshi a Madina tun farkon soma azumin watan Ramadan, kamar yadda kamfanin dillacin labaran ƙasar ya ruwaito.

Hukumomin kasar suka ce sun ɗauki matakai na lafiya sakamakon yawan masu ibadah a bana.

Har wa yau, suka ce ya zuwa yanzu babu ɓarkewa wata annoba ko cuta ko wani abin da ke barazana ga lafiya.

Hukumomin sun ce ma’aikata 18,000 ke aikin kula da masu ibadah a Masallacin kamar yadda BBC suka ruwaito.

Leave a Reply