Labarai

Mahara Sun Kashe ’Yan Sanda 3 A Kogi

An kashe ’yan sanda uku a wani hari da wasu da ake zargin ’yan bindiga ne suka kai ofishin ’yan sanda da ke Karamar Hukumar Adavi ta Jihar Kogi da sanyin safiyar Asabar.

Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kogi ta ce bata-garin sun far wa ofishin ne ta dama da hagu suna harbi babu kakkautawa, amma ’yan sanda suka fatattake su.

“Abin takaici, ’yan sanda uku sun rasu a musayar wutar, bata-garin kuma suka tsere da raunukan harbi a jikinsu ba tare da sun samu shiga ofishin ’yan sandan ba,” inji kakakin rundunar, SP William Ovye.

Sanarwar da ya fitar a safiyar Asabar ta ce Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar Kogi, Edward Egbuka,  ya tura jami’ai na musamman don tabbar da doka da oda a yankin tare da kamo maharan su girbi abin da suka shuka.

SP Ovye ya bukaci mazauna yankin da makwabtansu da su sa ido sosai, duk wanda suka gani da raunin harbi su hanzarta sanar da jami’an tsaro.

Ya ce kwamishinan ’yan sandan jihar ya ba da umarnin gudanar da cikakken bincike nan take, bisa jagorancin Mataimakin Kwamishian ’Yan Sanda Mai Kula da Binciken Manyan Laifuka.

Leave a Reply