Labarai

Saurayi Da Budurwa Sun Daurawa Kansu Aure A Jigawa

Wasu matasa sun daurawa abokinsu aure da budurwarsa ba tare da sanin iyayensu ba. Wannan al’amari mai kama da al’amara ya faru ne a unugwar Gandun Sarki cikin karamar hukumar Mallam Madori a jihar Jigawa.

Matashin mai suna Yahaya Isa wanda aka fi sani da Badi, kamar da wasa yace idan budurwar ta amince su yi aure yanzu ma ga sadaki a hannunsa.

Nan take kuwa budurwar mai suna Sa’a ta ce, ta amince su yi aure. Anan ne abokai suka hadu aka daura auren har ma aka bayar da sadakin N15,000 da zimmar za a ciko N35,000 a matsayin kudin sadaki.

Sheik Yusuf Abdurrahman, Limamin masarautar Hadejia na daga cikin malaman addinin da suka bada fatawar cewa aure ya dauru.

Jaridar Leadership