Latest:
Labarai

Mutum 76 sun shiga hannun jami’an tsaro bisa yunkurin auren jinsi a Gombe

Rundunar tsaro ta Civil Defence Corp a Nijeriya ta ce ta kama akalla mutum 76 da ake zargi da yunkurin yin auren jinsi a Jihar Gombe da ke arewa maso gabashin kasar.

Mai magana da yawun rundunar reshen Jihar Gombe SC Buhari Sa’ad ne ya bayyana haka a ranar Lahadi inda ya ce sun samu nasarar kama matasan ne bayan sun samu bayanan sirri cewa suna shirin wani biki na zagayowar ranar haihuwa da kuma auren jinsi.

Sa’ad ya shaida wa manema labarai cewa cikin mutu 76 da ake zargi, 59 maza ne inda 21 daga cikinsu suka tabbatar da cewa su ‘yan luwadi ne sai kuma akwai mata 17 wadanda aka kama a wurin.

Ya ce da zarar an kammala bincike za a gurfanar da waɗanda ake zargi a gaban kotu.

Ba wannan ne karon farko da ake kama masu auren jinsi ba a Nijeriya domin ko a watan Yulin bana sai da hukumar Hisbah ta Jihar Kano ta kama wasu da ake zargi da auren jinsi.

Haka ma a watan Agustan da ya gabata rundunar ‘yan sandan Jihar Delta ta kama sama da mutum 100 wadanda ake zarginsu da auren jinsi.

TRT Afrika Hausa