Daga Zainab Faruq
Uwargidan Gwamnan Jihar Bauchi, Hajiya Aisha Bala Abdulkadir Mohammed, ta kaddamar da rabon maganin Azithromycin ga yara âyan shekaru 1 zuwa 59 wata, a wani mataki na rage yawan mace-macen yara Æanana a fadin jihar.
An gudanar da bikin Æaddamarwar a garin Bauchi ranar Litinin, wanda ya nuna fara aiwatar da aikin ÆarÆashin shirin SARMAAN II. Aikin na gudana ne ÆarÆashin hadin gwiwar Hukumar BunÆasa Lafiyar Firamare ta Jihar Bauchi (BSPHCDA), tare da Mitosath da sauran abokan hulÉa na ci gaba.
A jawabin ta yayin bikin, Hajiya Aisha ta bayyana wannan shiri a matsayin muhimmin mataki wajen yakar cututtukan yara kamar su cutar numfashi, gudawa, trachoma da sauran cututtuka da ke addabar yara Æanana. Ta bayyana cewa gwamnatin jihar Bauchi na da Æwarin guiwa wajen ba da fifiko ga lafiyar mata da yara, inda ta jaddada cewa gwamnatin ta riga ta biya kuÉaÉen da ake buÆata don aiwatar da muhimman shirye-shiryen lafiya kamar ciyar da yara, shirin tsara iyali da kuma ayyukan lafiyar firamare.
âIna da kwarin guiwar tallafa wa irin waÉannan shirye-shiryen da ke canza rayuwa, musamman ma domin inganta lafiyar mata da yara,â in ji Hajiya Aisha, wadda ita ce shugabar gidauniyar Almuhibba Foundation. Ta kuma bayyana cewa gidauniyar ta bayar da guraben karatu 50 ga âyan mata da ke karantar Ilimin Nas da sauran fannoni a Jamiâar Almuhibba, a kokarin Æarfafa bangaren lafiyar jihar.
Uwargidan Gwamnan ta yabawa Mitosath, Cibiyar Binciken Lafiya ta Æasa (NIMR), Solina, eHealth Africa da Gates Foundation bisa goyon bayan da suke bayarwa wajen bunÆasa tsarin kiwon lafiya a jihar. Ta kuma yi kira ga shugabannin kananan hukumomi da matansu, sarakuna da malaman addini da su taimaka wajen wayar da kan iyaye da masu kula da yara domin tabbatar da cewa duk yara masu cancanta sun amfana da maganin.
Ta tabbatar wa alâumma cewa maganin Azithromycin lafiyayye ne kuma yana da tasiri, inda ta roÆi jamaâa da su ba da haÉin kai ga Æungiyoyin da za su rika yawo gida-gida domin rabon maganin.
A nasa jawabin, Kwamishinan Lafiya da Jin DaÉin Jamaâa na jihar, Dr. Sani Muhammad Dambam, ya bayyana cewa Azithromycin na da amfani wajen kare yara daga cututtuka da dama da kan kashe su da wuri, ciki har da cutar huhu, gudawa da trachoma. Ya kuma tabbatar da cewa maâaikatar lafiyar jihar za ta ci gaba da haÉin gwiwa da kungiyoyin tallafi domin samar da ingantattun ayyukan lafiya a fadin jihar.
Haka zalika, Shugaban Hukumar Lafiya ta Firamare ta Jihar Bauchi, Dr. Rilwanu Mohammed, ya bayyana cewa rabon maganin zai gudana ta hanyar yawo gida-gida, kuma zai Éauki tsawon kwanaki biyar. Ya bayyana fatansa cewa wannan mataki zai taimaka matuÆa wajen rage mace-macen yara a jihar.
Wakilan Maâaikatar Lafiya ta Tarayya, Hukumar Raya Lafiyar Firamare ta Æasa, Gates Foundation da Mitosath sun gabatar da saÆonnin ban girma inda suka jaddada aniyar su na ci gaba da tallafa wa jihar Bauchi wajen inganta harkar kiwon lafiya.
Rabon maganin Azithromycin yana Éaya daga cikin matakan da ke da nufin rage yawan mace-macen yara da inganta lafiyar alâumma, musamman a yankunan da ke da buÆatar kulawar lafiya ta musamman.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.









