Daga Zainab Kasim Ibrahim
Rundunar Yan Sandan Jihar Bauchi ta kama wasu matasa biyu da ake zargi da sace wayoyin lantark a yankin Dan Dango, da ke Bauchi.
Wadanda ake zargin su ne Adamu Abdullahi, mai shekaru 25, daga Dan Dango, da kuma Mujahid, mai shekaru 22, daga Gudum Hausawa, inda aka gabatar da su a shelkwatar ’yan sandan da ke Bauchi.
A lokacin da ake tuhumarsu, Adamu Abdullahi ya bayyana cewa wani mutum mai suna Haruna daga Gudum Hausawa ne ya umarce su da su yanke wayoyin wutar lantarki domin sayar da su a matsayin kayan gwangwan. Ya kara da cewa suna sayar da wayoyin a kan Naira Dubu daya kowanne kilo.
Shi kuwa Mujahid ya ce wannan shi ne karo na farko da ya shiga aika-aikar, saboda rashin kudi da rashin aikin yi. Ya ce Haruna ne ya jawo shi, amma bai taba shiga cikin transformer ko satar amocable ba. Ya bayyana nadama matuka, inda ya kira aikata laifin a matsayin “kus-kure da tsautsayi.”
Mai magana da yawun ’yan sandan jihar Bauchi, CSP Ahmed Mohammed Wakil, ya tabbatar da cafke su, yana mai cewa satar wayoyin wutar lantarki na gwamnati na jefa rayukan jama’a da kuma na masu laifin cikin hadari. Ya ce bincike na ci gaba da gudana don kamo sauran wadanda ke da hannu, musamman Haruna, sannan za a gurfanar da su a kotu bayan kammala bincike.
Rundunar ta yi kira ga jama’a da su kasance masu lura tare da kai rahoton duk wani motsi da ake zargi a kusa da kayayyakin gwamnati.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








