Lauyan kare hakkokin bil’adama Femi Falana ya bayyana matakin kamfanin mai ta Æasa NNPCL na Æara farashin litar mai a matsayin saÉa doka.
Yayi jawabi ne a gefen taron gaggawa da Æungiyar Æwadago tayi da majalisar zartaswar ta a birnin tarayya Abuja.
Mista Falana yace kamfanin NNPCL a matsayinsa na kamfani mai zaman kansa a yanzu bashi da Æarfi da ikon Æara kuÉin Man fetur take.
Ya kuma bukaci gwamnatin tarayya data koma ta sake nazarin hanya mai bullewa don magance matsalar, Éaya daga cikin hanyoyin acewarsa shine a magance matsalar Æarfin Dalar Amurka akan tattalin arzikin Najeriya.
Falana ya kuma ce al’ummar Najeriya zasu kalubalanci wannan tsari yana mai cewa mafita akan matsalar Man Fetur ya kunshi na doka da kuma siyasa.
Discover more from Albarka Radio
Subscribe to get the latest posts sent to your email.








